Janar Taoreeq Lagbaja ya rasu yana da shekaru 56.

Babban kwamandan sojojin Najeriya, kuma shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, ya sanar da mutuwar Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja, babban hafsan sojin kasar mai kimanin shekaru 56.

Spread the love

Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar dauke da sa hannun Bayo Onanuga ta ce Lagbaja ya rasu ne a daren ranar Talata a Legas bayan ya yi fama da rashin lafiya.

An haifi Laftanar Janar Lagbaja a ranar 28 ga Fabrairu, 1968, Shugaba Tinubu ya nada shi matsayin hugaban Hafsan Soja a ranar 19 ga Yuni, 2023, .

Aikinsa na soja ya fara ne a lokacin da ya shiga makarantar horas da sojoji ta Najeriya a shekarar 1987. A ranar 19 ga Satumba, 1992, aka ba shi mukamin Laftanar na biyu a rundunar sojojin Najeriya.

A duk tsawon hidimar sa, Laftanar Janar Lagbaja ya nuna jagoranci na kwarai da jajircewa, inda ya yi aiki a matsayin kwamandan runduna ta 93 da kuma bataliya ta musamman ta 72.

Ya taka muhimmiyar rawa a ayyukan tsaro na cikin gida da dama, ciki har da Operation ZAKI a jihar Benue, Lafiya Dole a Borno, Udoka a Kudu maso Gabashin Najeriya, da kuma Operation Forest Sanity a fadin jihohin Kaduna da Neja.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button