Jam’iyyar PDP reshen jihar Kebbi ta zargi gwamnatin APC a jihar
Jam’iyyar PDP reshen jihar Kebbi ta zargi gwamnatin APC a jihar da barnatar da dukiyar al’umma wajen tafiye-tafiye kasashen waje.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a, na jamiyyar Sani Dododo, ta ce a mai makon kashe kudaden jihar wajen sa ka hannu jari a kasashen waje kamata gwamnatin jihar ta yi amfani da su wajen samar da cigaba a jihar.
Jam’iyyar ta ci gaba da cewa, samar da yanayi mai kyau a jihar wajen inganta makamashi, zai jawo hankulan masu zuba jari a jihar.