Jamiyyar APC ta ciyo bashin Naira biliyan 5bn domin rantsar da Okpebolo – Obaseki

Spread the love

Gwamnan jihar Edo mai barin gado, Godwin Obaseki ya yi zargin cewa jam’iyyar APC ta ciyo bashin Naira biliyan 2 zuwa Naira biliyan 5 don gudanar da bikin rantsar da zababben gwamnan jihar, Sanata Monday Okpebolo, wanda aka shirya gudanarwa a ranar 12 ga watan Nuwamba.

Obaseki ya bayyana hakan ne a Benin a yayin kaddamar da kwamitin riko na jam’iyyar PDP reshen jihar.

Ya koka da cewa a matsayinsa na gwamna mai barin gado, jam’iyyar APC ba ta gayyace shi zuwa bikin rantsar da sabon gwamnan ba.

Ya kuma tabbatar wa da ‘ya’yan jam’iyyar cewa ba zai bar jam’iyyar PDP ba zai ci gaba da zama a jam’iyyar domin bayar da shawarwari.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button