Jam’iyar APC a Jahar Oyo ta bayyana shirin kwato mulki daga PDP a 2027.

Spread the love

Jam’iyyar APC reshen jihar Oyo ta bayyana cewa a shirye ta ke ta kokawa  mulki daga jam’iyyar PDP mai mulki a jihar a shekarar 2027.

Shugaban riko na jam’iyyar a jihar, Alhaji Olayide Abas, wanda ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga wasu shugabannin jam’iyyar daga kananan hukumomi shida na shiyyar Ibadan Outer City, ya sha alwashin cewa APC a shirye take ta rusa PDP domin kwato gidan gwamnatin Agodi.

Ya kuma ba da tabbacin cewa jam’iyyar za ta dawo mulki ta hanyar kwato kujerar gwamna daga hannun jam’iyya mai mulki a jihar.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button