Jami’an Civil Defence sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

mayaƙan Boko Haram

Spread the love

Rundunar tsaro ta Civil Defence da ke Najeriya, ta ce mayakan Boko Haram sun yi wa tawagar jami’anta da ke sintirin baiwa turakun babban layin wutar lantarkin Shiroro kariya, kwanton ɓauna a jihar Neja.

  • http://Rfi hausa c tace a wata sanarwar da kakakin rundunar Babawale Afolabi ya fitar a yammacin jiya Talata, lamarin ya faru ne a garin Farin Kasa da ke kusa da ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Sanarwar ta ce tawagar na kunshe ne da manyan jami’ai 71 da suka fito daga sassan rundunar daban daban, lokacin da mayaƙan masu iƙirarin jihadi su sama da dari 2 suka kai musu hari, a lokacin da suke dawowa daga mahaƙar ma’adinai.

A cewar sanarwar, duk da kwanton ɓaunar da makayan Boko Haram suka yiwa jami’an na Civil Defence, sai da suka samu nasarar kashe sama da mayaƙan Boko Haram 50, a musayar mutar da suka yi.

Kakakin rundunar ya kuma tabbatar da cewa jami’ansu 7 sun samu raunuka, inda yanzu haka suke samun kulawa a wani asibiti da ke cikin garin Kaduna, sannan wasu 7 kuma sun ɓace inda ake ci gaba da nemansu.

An dai tura da tawagar rundunar Civil Defence ne don sanya ido tare da samar da kariya ga turakun layukan wutar lantarki, sakamakon yawaitar hare-hare da lalatasu da ake yi, wanda ke haifar da katsewar wutar lantarki a faɗin ƙasar.

 

Gwamnatin Sokoto ta tabbatar da mutuwar mutane 25 sanadiyar cutar amai da gudawa

Jami'an Civil Defence sun kashe mayaƙan Boko Haram 50
Cutar kwalara jihar Sokoto

Mahukuntan jihar Sokoto da ke shiyar Arewa maso Yammacin Najeriya, sun tabbatar da mutuwar akalla mutane 25 sakamakon barkewar cutar amai da da gudawa.

Kwamishinar Lafiya ta Jiha Sakkwato, Hajiya Asabe Balarabe ta bayyana cewa mutum dubu daya da 160 ne annobar ta shafa, inda 25 suka suka rasu, wasu 15 kuma na kwance a asibiti.

Kwamishiniyar ta ce an samu ɓullar cutar ce a ƙananan hukumomin Sokoto ta Arewa da Silame da Kware, inda ta ce yazuwa yanzu an ɗauki matakan dakile yaɗuwarta.

Yadda zargin cin zarafin ma’aikata ke kara yawa akan dillalan man fetur a Najeriya

Yayin da manyan dillalan man fetur a Najeriya ke fafutuka koda yasuhe wajen kwato hakkokinsu daga gwamnati, a bangare guda kuma ana zarginsu da musgunawa wadanda ke aiki a karkahsin su, musamman direbobi da kuma masu sayar musu da man. Wakilinmu a Yola Ahmad Alhassan ya aiko mana da rahoto a kai.

Aƙalla mutane 25 cutar kwalara da aka fi sani da amai da gudawa tayi ajalinsu a jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya.

Rahotanni sun ce cutar ta ɓarke a ƙananan hukumomi 3 na jihar, kuma zuwa yanzu an sami rahoton mutane 1,160 da cutar ta kama.

Kwamishiniyar Lafiya ta jihar Asabe Balarabe, ce ta bayyana hakan lokacin da take zantawa da manema labarai.

Kwamishiniyar ta kuma yi ƙarin hasken cewa zuwa yanzu ana kan kula da mutane 15 a da ke kwance a asibiti, waɗanda suka fito daga ƙanana hukumomin Sokoto ta arewa da Silame da kuma Kware.

Bayanai sun nuna cewa tuni jama’a suka fara tururuwar zuwa ɗakunan gwajin lafiya musamman mata masu juna biyu da kuma ƙananan yara, matakin da kwamishiniyar ta yaba da shi ƙwarai da gaske.

Katu ta wanke Kwamishina kan zargin lalata da matar aure 

Lalata da matar aure
Kwamishina a jihar Jigawa

Zargin kula matar aure: Gwamna Namadi ya janye dakatarwar da ya yi wa Kwamishinansa bayan kotu ta wanke shi

Gwamna Malam Umar Namadi ya dage dakatarwar da aka yi wa Kwamishinan ayyuka na Musamman, Auwalu Dalladi Sankara, daga yanzu nan take.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya sanyawa hannu.

“Za a iya tunawa cewa an dakatar da kwamishinan bisa zargin da ake yi masa kan faruwar wani al’amari daga rahotan hukumar Hisbah ta jihar Kano”, inji Sakataren Gwamnatin.

Sanarwar ta ce an dage dakatarwar ne bayan kotu ta wanke Kwamishinan.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button