Iyayen daliban Zamfara da suka makale a kasar Cyprus suna rokon gomna Lawal ya ceto su
Iyayen daliban jihar Zamfara da ke karatu a jami’ar Cyprus International University karkashin tallafin gwamnati suna rokon gwamna Dauda Lawal da ya magance wahalhalun da ‘ya’yansu ke ciki sakamakon rashin biyansu tallafin karatu.
Daliban Zamfara 93 ne gwamnatin da ta gabata ta dauki nauyin karatunsu a jami’ar da ke kasar Cyprus.
Sai dai a yanzu suna fuskantar kalubale mai tsanani, bayan da aka kore su daga gidajen kwanansu da kuma hana su samun kayan aiki masu mahimmanci saboda makudan kudade.
Wani Uban da abin ya shafa, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce hukumar jami’ar na cin zarafin yaron sa da sauran su kan basussukan da ba a biya su ba.
A lokacin da gwamnatin da ta shude ta tura ‘ya’yanmu kasashen waje, mun yi imanin komai zai gudana lami lafiya. Amma a ‘yan kwanakin nan, an kori ‘ya’yanmu daga matsuguninsu inji shi.
Wasu dalibai, musamman maza, sun rungumi sana’o’in da ba su dace ba, don tallafa wa kansu, lamarin da iyaye ke ganin ya hana su karatu.
Wani daga cikin iyaye, wanda shi ma ya zabi a sakaya sunansa, ya soki gwamnati mai ci a kan gazawa wajen warware matsalar kudi, duk da ikirarin kokarin da take yi.