Isra’ila ta kai hare-hare ‘sama da 300’ a Syria bayan kifar da gwamnatin Assad
Rahotanni sun nuna cewa jiragen sama na Isra'ila sun kai ɗaruruwan hare-hare ta sama a Syria, ciki har da Damascus babbn birnin ƙasar.
Rahotanni sun nuna cewa jiragen sama na Isra’ila sun kai ɗaruruwan hare-hare ta sama a Syria, ciki har da Damascus babbn birnin ƙasar.
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’adam ta Syrian Observatory for Human Rights (SOHR) mai mazauni a Birtaniya ta tattara sama da hare-hare 310, waɗanda dakarun IDF suka kai tun bayan kifar da gwamnatin Assad a ranar Lahadi.
Hare-haren sun mayar da hankali ne kan kadarorin sojin Syria, ciki har da ma’ajiyar makamansu da filin jirgin sama da cibiyoyin bincike.
Isra’ila ta ce tana kai hare-haren ne domin hana makamai faɗawa “hannun masu tsattsauran ra’ayi” a Syria.
Ƙungiyar SOHR ta ce hare-haren sun fi ƙamari a Aleppo da Damasucs da Hama, kuma ko a daren Litinin kaɗai an kai sama da hare-hare 60.
Rahotannin sun ce an lalata duk wuraren da aka kai hare-haren.
BBC ta tantance bidiyon wasu daga cikin hare-haren, daga cikinsu kuma ciki har da wani wanda aka kai a sansanin sojin ruwa da ke Latakia.
Rami Abdul Rahman, shi ne shugaban SOHR kuma ya kwatanta hare-haren da yunƙurin “kassara sojin Syria”.
IDF ta ƙaryata labarin, inda ta shaida wa BBC cewa labarin hare-harenta a Damascus “ƙarya ne.”
A ranar Litinin, rundunar sojin Isra’ila ta saki waso hotunan lokacin da sojojinta suke tsallake tuddan golan da ta mamaye domin shiga Syria ta yankin raba-grdama da dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniye suke aiki.
Ƙwace iko da Isra’ila ta yi ɓangaren Syria na yankin, “wani yunƙuri ne na wucin gadi har zuwa lokacin da za a samu tsari mai kyau,” in ji firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu.
“Idan muka tabbatar da aminci daga maƙwabtanmu musamman shugabannin Syria na yanzu, za mu yi farin ciki. Amma idan ba mu samu ba, za mu yi duk abin da za mu iya domin kare Isra’il,” in ji shi a ranar Litinin.
Ma’aikatar harkokin wajen Turkiyya ta soki hare-haren na Isra’ila a yankin, inda ta zargi Isra’ila da yunƙurin “mamaye a lokaci mai muhimmanci da ake gani za a samar da tabbataccen zaman lafiya ga mutanen Syria suke nema na tsawon shekaru.”
Yankin raba-gardamar, na cikin yarjejeniyar tsagaita wuta da aka yi tsakanin Isra’ila da Syria shekarar 1974 domin raba tsakanin dakarun Syria da Isra’ila bayan da farko Isra’ila ta ƙwace iko da tuddan golan.
Amma sai Isra’ila ta mayar da golan ƙasarta a shekarar 1981, amma ƙasashen duniya ba su amince da matakin ba, duk da cewa Amurka ta amince a shekarar 2019.
Da aka tambaye shi ko IDF ta kai hare-hare a daren Litinin, ministan harkokin wajen Isra’ila Gideon Saar ya ce Isra’ila ta fi damuwa ne kan kare ƴanƙasarta.
“Shi ya sa muka kai hari a wurare masu muhimmanci, kamar misali sauran wuraren da aka haɗa makaman sinadari da makamai masu linzami masu cin dogon zango da rokoki domin gudun kar su faɗa hannun masu tsautsauran ra’ayi,” in ji shi.
A ranar Litinin, kwamitin sa ido kan makaman sinadarai ya gargaɗi Syria kan tabbatar da cewa cibiyoyin haɗa makaman na sinadarai ba a taɓa su ba.
Hare-haren Isra’ila sun zo ne bayan ƴantawayen Syria sun ƙwace babban birnin Syria, Damascus, sannan sun kifar da gwamnatin Bashar al-Assad a ƙarshen mako, inda shi da mahaifinsa suka mulki ƙasar tun shekarar 1971.
Mayaƙa ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar Hayat Tahrir al-Sham (HTS) ne suka kutsa Damascus a ranar Lahadi, kafin daga bisani suka bayyana a talabijin na ƙasar, inda suka sanar da cewa sun ƙwace mulkin ƙasar.
Yahaya Bello ya kunyata jam’iyyar mu – matasan Vanguard na APC
Jam’iyyar matasan Vanguard ta APC ta gargadi tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello da ya daina tozarta jam’iyyar kan yakin da yake yi da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar matasan, Rasheed Sanusi, kungiyar ta yi mamakin dalilin da ya sa tsohon gwamnan ya bijire wa shari’a tare da kawo wa jam’iyyar kunya.
Kungiyar ta Youth Vanguard ta bukaci Bello da ya bi tafarkin karramawa ya mika kansa domin ya yi la’akari da lokacin da ya yi a kan mulki da kuma kare jam’iyyar da fadar shugaban kasa daga kara kunya, musamman ganin yadda aka kame tsofaffin gwamnonin jam’iyyar adawa. Jam’iyyar People Democratic Party (PDP) ta EFCC.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, A halin yanzu ana yin mummunar fassara da rashin biyayyar sammacin da Bello ya yi na sammaci na kotu da cin kasuwa, sakamakon kariyar da fadar shugaban kasa ta yi a matsayin dan jam’iyyar APC da kuma taka rawa a kwamitin yakin neman zaben Tinubu/Shettima.
Rashin taimakon da mai magana da yawun shugaban kasar ya bayyana kwanan nan a cikin wata hira da gidan talabijin ba shi da wani taimako ko karba.
An jiyo Orji Uzor Kalu yana cewa ‘Ina da wata kara da EFCC. Na bayyana a dukkan shari’ar da ake yi a kotu tsawon shekaru 12, ban taba guduwa ba, kuma ban taba tsallake wani zaman kotu ba. Ni ba irin mutumin da zai yi watsi da zaman kotu ba.
Hukumar EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku, bisa zarginsa da ayyukansa da ayyukan da ya yi a lokacin da yake kan karagar mulki, kuma tuni aka bayar da belinsa.
A makon da ya gabata ne dai aka kama tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, tare da bayar da belinsa.
Har ila yau, gwamnan jihar Edo mai barin gado, Mista Godwin Obaseki ya bayyana shirinsa na amsa gayyatar EFCC, idan an gayyace shi.
To, me yasa Yahaya Bello ke kin sammacin kotu? Su wane ne wadanda ake zargin sun baiwa Bello kariya? Wannan halin da ake ganin na rashin taimako abin kunya ne ga Jam’iyyar mu da fadar Shugaban kasa da ma kasa baki daya. Abin kunya ne a duniya.
Muna rokon Bello da ya fito da radin kansa domin gurfanar da shi a gaban kotu ko kuma a tilasta masa yin hakan ta hanyar hadin gwiwa tsakanin hukumomi. Ya isa ya isa.