Hukumar zabe ta kasa ta maye gurbin Ebiseni da Festus a zaɓen jihar Ondo
Hukumar zabe ta kasa ta maye gurbin Ebiseni da Festus a matsayin dan takarar jam'iyyar LP
Gabanin zaben gwamnan jihar Ondo na ranar Asabar, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta maye gurbin dan takarar jam’iyyar Labour, Olusola Ebiseni da Dr. Olorunfemi Ayodele Festus.
Hukumar ta ce an maye gurbin shi ne bayan an ba ta takardar shaidar da kotun daukaka kara ta yanke wanda ya yi watsi da hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a shafin X na hukumar a ranar Juma’a.
Wata babbar kotun tarayya mai lamba FHC/ABJ/CS/1105/2024, a ranar 27 ga Satumba, 2024, ta umurci INEC da ta amince da Olusola Ebiseni a matsayin dan takarar jam’iyyar Labour Party (LP) a zaben gwamnan jihar Ondo a 2024.
“Duk da haka, a daukaka kara mai lamba CA/ABJ/CV/1172/2024 da kungiyar kwadago ta shigar, kotun daukaka kara da ke Abuja ta yi fatali da hukuncin da FHC ta yanke na rashin hurumi.
“A bisa bin umarnin kotu, hukumar ta dawo da Olorunfemi Ayodele Festus, wanda aka fara buga sunansa a matsayin dan takarar gwamnan jihar Ondo a shekarar 2024, sannan kuma aka saka shi a shafinmu na yanar gizo domin samun bayanan jama’a,” in ji sanarwar.
Da yake tofa albarkacin bakinsa, Sakataren Yada Labarai na LP, Obiorah Ifoh, ya ce Ebiseni shi ne dan takarar da kungiyar NLC ta fitar a jam’iyyar, amma kotun daukaka kara ta kore shi yayin da ta dawo da “Dan takara mai inganci,” Dr Olorunfemi.