Hukumar zabe ta kasa INEC ta tabbatar da gudanar da zaben gomna a jihar Ondo
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta shirya tsaf domin gudanar da zaben Gwamnan Jihar Ondo a ranar Asabar 16 ga watan Nuwamba, Shugaban Hukumar Farfesa Mahmood Yakubu shine ya tabbatar da hakan.
Da yake jawabi a gaban a taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Dome da ke Akure, Jihar Ondo a ranar Alhamis 7 ga watan Nuwamba, Farfesa Yakubu ya kuma tabbatar da cewa za a tura na’urar tantance masu kada kuri’a (BVAS) don tantance masu kada kuri’a a rumfunan zabe da kuma masu kada kuri’a.
Ya ce Hukumar ta amince wa kungiyoyi 111 na cikin gida da na kasashen waje wadanda suka tura wakilai 3,554 a matsayin masu sa ido, sannan kungiyoyin yada labarai sama da 100 sun tura ma’aikata 700 ciki har da ‘yan jarida mata 129.
An shirya duk takardar shaida da tambarin jam’iyun siyasa kuma za a tattara su a ofishin INEC na jihar Ondo.
Shugaban na INEC ya bayyana cewa ayyuka biyu ne suka rage kafin ranar zabe: ranar yakin neman zaben da zai kare da tsakar daren ranar Alhamis 14 ga watan Nuwamba da kuma zaben kansa.
Farfesa Yakubu ya bayyana cewa hukumar tare da hadin gwiwar jami’an tsaro sun samar da kwararan matakan tsaro domin kare masu kada kuri’a, da ma’aikatan hukumar zaben, da masu sa ido, da ma’aikatan yada labarai a duk wuraren da ake tattara sakamakon zabe.
A cewarsa, Sufeto-Janar na ‘yan sanda da sauran hukumomin da abin ya shafa sun ba da tabbacin samar da ingantaccen yanayi don ba da damar shiga ba tare da cikas ga duk masu ruwa da tsaki a harkar zabe ba.