Hukumar tsaron farin kaya ta aike da dakarunta dubu 6,000 gabannin zaɓen jihar Ondo
Hukumar tsaron farin kaya ta aike da dakarunta dubu 6,000 da jiragen ruwa gabannin zaɓen jihar Ondo
Gabanin zaben gwamnan jihar Ondo da za a gudanar a ranar 16 ga watan Nuwamba, rundunar sojin ruwa ta Najeriya ta tura jiragen ruwa domin kare muhimman kayayyakin zabe da jami’ai a yankunan jihar, musamman a yankunan masu kogi.
Kyaftin Aliyu Usman, Kwamandan Rundunar Sojojin Ruwa ta Najeriya Igbokoda, ya bayyana hakan a ranar Litinin din nan cewa za su inganta tsaro domin kare al’ummomin bakin kogi da kuma kan iyakokin kasar a ranar zabe.
Usman ya bayyana muhimmancin tabbatar da inganta hanyoyin ruwa da ake amfani da su wajen jigilar ma’aikatan INEC da kayayyakin zuwa wuraren zabe.
Hakazalika, kwamandan hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (NSCDC), Ahmed Audi, ya bayar da umarnin tura jami’ai maza da mata 6,000 domin samar da isasshen tsaro a lokacin zaben.
CG Audi ya ce hukumar NSCDC a shirye take don tabbatar da gudanar da sahihin zabe, tare da lura da cewa jami’an da aka zabo daga jihar mai masaukin baki, jihohi makwabta, da hedkwatar kasa sun hada da Special Female Squad, Counter Terrorism Unit (CTU), Agro Rangers Unit. , Chemical, Biological, Radiological, Nuclear, and Explosive Unit (CBRNE), K-9 Unit, Marine Unit, CG’s Mining Marshall, Sashin Kula da Zabe (EMU), da kuma Sashen Hankali da Bincike.
A baya dai rundunar ‘yan sandan ta sanar da tura jami’anta 22,239 domin gudanar da babban zaben jihar.