Hezbollah ta kai hare-hare kan sansanoni sojojin Isra’ila
Yaƙin da Isra’ila ke yi a Gaza — wanda a yanzu ya shiga kwana na 407 — ya kashe aƙalla Falasɗinawa 43,764 da jikkata 103,480, kuma ana fargabar 10,000 suna binne a ƙarƙashin ɓaraguzai. A Lebanon ma, Isra’ila ta kashe mutum 3,440 tun Oktoban bara.
Wata mata tana jimami a lokacin da take ɗauke da gawar ɗanta da aka kashe a hare-haren Isra’ila a unguwar Sheikh Ridwan.
Isra’ila ta kashe Falasɗinawa 11 ta jikkata wasu da dama a ruwan bama-bamai da ta yi kudanci da arewacin Gaza, a cewar rahoton kamfanin dillancin labarai na WAFA.
Kamfanin dillancin labaran na Falasɗinawa ya ce masu mamaya na Isra’ila sun kashe fararen hula huɗu sun kuma jikkata da dama a hare-haren da suka kai unguwar al-Karama a arewacin Birnin Gaza.
Sojojin na Isra’ila sun kuma kashe wasu mutanen biyu sannan sun jikkata wasu bayan sun jefa bam wani gida a unguwar Zeitoun dake kudu maso gabshin birnin.
Kamfanin dillancin labaran ya ƙara da cewa sojojin Isra’ila sun harbe wani matashi lokacin da yake yunƙurin guduwa daga arewacin Gaza zuwa tsakiyar birnin, don kauce wa yankin da aka killace.
A kudancin Gaza kuwa, masu aikin ceto sun ton gawawwakin wasu fararen hula huɗu da aka kashe a hare-haren Isra’ila ta sama a wurare daban-daban a Rafah.
Hezbollah ta kai hare-hare kan sansanoni sojojin Isra’ila
Hezbollah ta sanar da kai hare-haren makaman roka da jirage marasa matuka kan sansanonin sojojin Isra’ila, da matsugunai da sojoji a arewacin Isra’ila da kudancin Lebanon.
Kungiyar ta Lebanon ta ce ta kai hare-hare 31 kan sojojin Isra’ila da sansanoninsu da kuma matsugunnensu.
Ta yi da’awar cewa mayakanta sun kai hari kan sansanin sojojin Isra’ila na Tirat Carmel a kudancin Haifa, da sansanin Shraga kusa da Acre, inda suka yi amfani da makaman rokoki da aka bunƙasa su.
Ta kuma ba da rahoton kai hari kan taron sojojin Isra’ila tara a kusa da Doviv da Sa’sa da Misgav da Yorn a arewacin Isra’ila.
Ƙari a kan haka, Hezbollah ta ce ta kai hari kan wuraren sojojin Isra’ila 19 a kusa da garuruwan Maroun al-Ras da Markaba da Khiyam da Hanine da Talloussah a Lebanon.
Gidan rediyon Isra’ila ya ce an gano aƙalla makaman roka 40 da kuma jirage marasa matuka uku waɗanda aka harbo su daga Lebanon zuwa kudancin Isra’ila, abin da ya sa aka kunna jiniyar hare-haren sama a arewacin Isra’ila.