Har yanzu akwai jihohi bakwai da ba su fara biyan mafi karancin albashi ba
Akalla jihohi bakwai da babban birnin tarayya ne suka gaza amincewa da mafi karancin albashin da wasu suka aka fara biya a watan Oktoban wannan shekara.
Hakan na zuwa ne yayin da jihohi 25 suka fara biya wasu kuma sun bayyana adadin da za su biya a matsayin mafi ƙarancin albashi.
Jihohin da har yanzu ba su amince da mafi karancin albashi ba, sun hada da Zamfara, Sokoto, Osun, Cross River, Imo, Plateau, Taraba, da FCT.
Jaridar PUNCH a ranar Asabar ta tattaro cewa biyan mafi karancin albashi na N70,000 na iya daukar lokaci mai tsawo a Zamfara, saboda har yanzu jihar tsohon mafi karancin albashi na N30,000 ta ke biya.
Har yanzu dai jihar ba ta fitar da wata sanarwa kan mafi karancin albashi na N70,000 ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Haka kuma, jihar Sokoto har yanzu ba ta fara biyan mafi karancin albashi ba duk da alkawarin da Gwamna Ahmed Aliyu ya yi na cewa gwamnatinsa za ta kasance cikin jihohin da za su fara yin hakan.
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta biya mafi karancin albashi, amma har yanzu jihar ba ta amince da wani adadi ko fara biyan mafi karancin albashi ba.
Jihar Cross River kuma ba ta amince da mafi karancin albashi na N70,000 ba.
A ranar 1 ga Mayu, 2024, Gwamna Bassey Otu na jihar ya sanar da N40,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi ga ma’aikatan gwamnati kafin mafi karancin albashi na N70,000.
A can jihar Imo ma Har yanzu dai mafi karancin albashin bai fara aiki ba, ko da yake Gwamna Hope Uzodimma ya tabbatar wa ma’aikata cewa gwamnatin sa ta dukufa wajen aiwatar da yadda albashin zai kasance.
A ranar 5 ga Satumba, 2024, Gwamna jihar Filato Agbu Kefas na jihar ya ce a shirye ya ke ya biya sabon mafi karancin albashin ma’aikatan, inda ya ce tuni shugaban ma’aikata da ma’aikata ke tattaunawa kan yadda za a aiwatar da shi.
Har yanzu ministan babban birnin tarayya Abuja Wike bai yi magana kan aiwatar da mafi karancin albashi ba zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Inda ma’aikata a fadin kasar nan ke cigaba da kokawa kan matsalar tattalin arziki da a ake fama da shi, ganin cewa yanzu Naira 70,000 ba ta isar magidanci.
Idan zaku iya tuna cewa kungiyar kwadago ta ce sun amince da mafi karancin albashi na N70,000 ne saboda alkawarin da Shugaba Bola Tinubu ya yi na ba zai kara farashin man fetur ba.
Shugaban kungiyar kwadago, Joe Ajaero, a ranar 20 ga watan Satumba, ya ce Tinubu ya musu alkawarin bazai kara Farashin man fetur ba wanda hakan ya sa suka amince da mafi karancin albashin na N70,000.
Ajaero ya yi nuni da cewa, tsadar man fetur din ya yi illa ga biyan mafi karancin albashi na N70,000 na kasa, inda ya bukaci gwamnati da ta gaggauta magance matsalolin yunwa da fatara da suka addabi ‘yan Najeriya.