Hankulan magoya bayan mawaka Davido, Wizkid, Burna Boy, ya rabu gida biyu
Magoya bayan sun raba hankulan su ta bangarori daban-daban biyo bayan sanarwar da aka fitar na wadanda aka zaba don lambar yabo takan bikin karrama mawakan kashi 67th, wanda aka fi sani da Grammys.
Wasu mawakan Najeriya sun fito cikin jerin sunayen, da suka hada da Davido, Wizkid, Burna Boy, Yemi Alade, Asake, Tems, Rema, da Lojay.
Ana zaben mafi kyawun Waƙar da ta yi fice a Afirka wadda suka haɗa da Yemi Alade’s ‘Gobe,’ Asake da Wizkid ‘MMS’ da Burna Boy’s ‘Higher.’ .
Wakar Rema’s ‘Heis’ da Tems’ mai taken ‘Born in the wild ‘ su ne wadda aka zaba a kundin wakoki mafi kyau a Duniya. Tems ya kasance kan gaba a jerin sunayen ‘yan wasan Najeriya da ke da mafi yawan adadin wadanda aka zaba don lambar yabo ta Grammy na 67, sai kuma ‘Burning’.
Magoya bayan sun yi ta muhawara a shafukan sada zumunta kan yadda kowannensu ya cancanci kyautar.