Haaland zai fi kowa albashi a Premier, Newcastle na nazarin sayar da Isak

Spread the love

Manchester City na da tabbacin ɗanwasanta na gaba Erling Haaland, mai shekara 24, zai sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya inda zai zama wanda ya fi albashi a gasar Premier.

West Ham na diba yiyuwar ɗauko ɗanwansa tsakiya na Manchester City da Ingila James McAtee, mai shekara 22, yayin da take fargabar rabuwa da Lucas Paqueta, na Brazil mai shekara 27 a Janairu January.

Ruud van Nistelrooy na neman aikin horar da ƴanwasa a Premier bayan barin Manchester United.

Kocin Luton Rob Edward zai iya barin ƙungiyar yayin da Coventry ke diba yiyuwar ɗauko shi.

Kocin Aston Villa Unai Emery na son ƙarfafa bayansa a Janairu inda yake son ɗauko ɗanwasan Diego Llorente, mai shekara 31 Real Betis amma kwangilar ɗanwasan ta dogon lokaci na iya zama cikas.

Haka ma Aston Villa na cikin masu ribibin ɗanwasan tsakina na Athletic Bilbao Oihan Sancet, mai shekara 24, amma babu tabbas ko za ta iya biyan farashinsa fam miliyan 66.

Juventus na diba yiyuwar ɗauko ɗanwasan gaba na Manchester United da Netherlands Joshua Zirkzee, mai shekara 23, yayin da makomar ɗanwasan ƙungiyar na Serbia Dusan Vlahovic, mai shekara 24, ke cikin rashin tabbas.

Duk ƙungiyar da ke son ɗanwasan gaba na Najeriya Victor Osimhen sai ta ware sama da fam miliyan 62 ga Napoli.

Newcastle za ta iya sayar da ɗanwasan Sweden Alexander Isak, mai shekara 25, domin amfani da kuɗin domin yin sabon zubi.

Ɗanwasan Jamus Jonathan Tah, mai shekara 28, ba zai sabunta kwangilar shi ba a Bayer Leverkusen inda ɗanwasan ke harin zuwa Bayern Munich ko Barcelona.

Ɗanwasan baya na Paris St-Germain Milan Skriniar, mai shekara 29, zai iya dawo wa Italiya a Juventus yayin da yake cin benci a Paris.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button