Gwamnatin Tarayya ta dakatar da dalibai 13 da suke cin zarafin  abokan karatunsu a jahar Enugu

Spread the love

Gamnatin tarayya ta bayar da umarnin dakatar da wasu dalibai 13 da ake zargin suna da hannu a cin zarafi da aka yi wa ’yan uwansu da ke makarantar sakandare (SS1) a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Enugu na tsawon makonni shida a ranar 7 ga Nuwamba.

Ministan Ilimi Dr. Maruf Alausa ya bayar da umarnin dakatarwar ne domin share fagen gudanar da cikakken bincike kan lamarin da kwamitin ladabtarwa da ma’aikatar ilimi ta tarayya ta kafa.

Umurnin ya biyo bayan yada wani faifan bidiyo mai tada hankali a shafukan sada zumunta, inda aka ga wasu gungun dalibai suna cin zarafin wani dalibin da aka gano cewa dalibin SS1 ne.

Darektan yada labarai da hulda da jama’a a ma’aikatar, Folasade Boriowo, a cikin wata sanarwa a ranar Laraba a Abuja, ta ce Dakta Alausa ya sake jaddada aniyar ma’aikatar wajen ganin an samar da ingantaccen yanayi na koyo a dukkan makarantun tarayya a fadin Najeriya.

Ya kuma tabbatar wa iyaye da masu riko da kuma sauran jama’a cewa za a yi duk abin da ya dace don dawo da zaman lafiya da kuma tabbatar da tsaron daliban FGC Enugu.

“Wani rahoto na baya-bayan nan da ma’aikatar ilimi ta tarayya ta samu ya yi nuni da irin yadda ake cin zarafi a Kwalejin Gwamnatin Tarayya (FGC), Enugu, wanda ya haifar da damuwa sosai game da tsaro da kuma da’a a cikin makarantun.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button