Gwamnatin tarayya na yin namijin kokari wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya

Spread the love

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana a ranar Talata cewa gwamnatin tarayya na yin namijin kokari wajen ganin ta shawo kan kalubalen tsaron kasar.

Tunji-Ojo wanda ya kasance bako a shirin Siyasar Gidan Talabijin na Channels a Yau, ya ce mai baiwa kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu; Ministan tsaro, Mohammed Badaru da babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Christopher Musa, sun rasa barci kan lamarin.

“Ba wanda yake hutawa. Ba NSA ba, Mallam Nuhu Ribadu, ba ministan tsaro ba, ba shugaban hafsan tsaro ba, ba hukumar DSS ba.” Inji Ministan.

“Ba wanda yake barci, muna aiki. Wannan batu na tsaro babban al’amari ne da ya shafi kasa baki daya, kuma ba zan zauna a nan na ki daukar nauyin tsaron ‘yan Nijeriya a madadin Shugaban kasa ba.”

Ya bayyana cewa duk da cewa an samu ingantuwar tsaro a kasar tun bayan hawan gwamnatin shugaba Bola Tinubu, ministan ya bayyana cewa sojoji sun durkusar da ‘yan ta’addan Boko Haram da kuma kungiyar Islamic State of West Africa Province (ISWAP).


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button