Sabuwar Shekara:Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara ta 2025
Sabuwar Shekara: Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar 26,27 ga watan Disamba da 1 ga watan Janairu na sabuwar shekara a matsayin ranakun hutu
Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Tarayya ta ayyana ranakun 25 da 26 ga watan Disamba, 2024, da kuma 1 ga watan Janairu, 2025, a matsayin ranakun hutu don bikin Kirsimeti, da kuma na sabuwar Shekara.
Sanarwa hakan ta fito ne cikin wata takarda da babban sakatare na ma’aikatar, Dokta Magdalene Ajani, ta sanya wa hannu.
Ministan harkokin cikin gida, Dokta Olubunmi Tunji-Ojo, a madadin Gwamnatin Tarayya, ya kirayi ‘yan Najeriya da su yi amfani da wannan lokaci na bukukuwa sabuwar shekara wajen tunawa da muhimmanci zaman lafiya, da hadin kai a tsakanin al’umma.
Gidan television na Channels ta rawaito cewa Dokta Tunji-Ojo y jaddada muhimmanci na wannan lokaci na bukukuwan, yana mai cewa yana da matukar muhimmanci wajen kyautata zumunci da dangantaka tsakanin iyalai da al’ummomi.
Labarai masu alaƙa
Kasafin kudi na 2025 ba zai magance tabarbarewar tattalin arzikin Najeriya ba – Atiku