Gwamnatin Nijar ta gayyaci kamfanoni Rasha a harkar tonon Uranium
Yayin da ake ci gaba da kai ruwa rana tsakanin Jamhuriya Nijar da Faransa game da wata muhimmiya mahakar Uranium da ke areawcin ƙasar, gwamnatin mulkin soji da ta kwace mulki daga hanun Bazoum Mohamed, ta shiga zawarcin ƙasar Rasha inda ta yi kira ga Moscow ta shigo a dama da ita.
A wata hira da kafar yada labarai ta Rasha Ria Novosti rana 13 ga wanan watan a daura da taron ministocin Rasha da Afirka a Sotchi, ministan kula da harkar ma’adinai ƙarƙashin ƙasa na Jamhuriya Nijar Ousmane Abarchi, ya yi kira ga kamfanonin Rasha da ke sha’awar aikin bincike da tono arzikin ƙarkashin ƙasa su ziyarci ƙasar.
Abarchi ya ƙara da cewa tuni suka gana da wasu daga cikin kamfanonin Rasha da suka nuna sha’awar su akai.
Da aka tambaye shi akan batun takaddamar su da Faransa, Ousmane Arbachi ya amsa da cewa:
Da yake Faransa ta bakin Shugaban ta bata amince da shugabanin da ke kan mulki amatsayin su na halastatu ba, ba muga dalilin zai sa mu cigaba da basu damar kwashe arzikin karkashin kasa da Allah ya albarci Nijar da shi.
Wannan matsayar dai na zuwa a daidai lokacin da kamfanin kula da albarkacin ƙarkashin ƙasa Sopamin ya bayyana adawar sa da shirin Orano na dakatar da ayyukan sa a arewacin ƙasar daga 31 ga watan Octoban da ya wuce.