Gwamnatin Kano za ta sabunta lasisin Mafarauta don kiyaye namun daji
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana za ta sabunta lasisin mafarauta a fadin jihar
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana shirin sabunta lasisin farauta a fadin jihar a wani bangare na kokarin kare namun daji da kare muhalli.
Ahmad Halliru Sawaba, mashawarci na musamman ga gwamna kan harkokin kare namun daji ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da manema labarai a Kano.
Ya ce kamata ya yi a rika sarrafa albarkatun namun daji a matsayin kadarorin jama’a, da doka ta tsara su, sannan a kai su ta hanyar takardar shedar da ta dace da aka samu ta hanyar rajista.
“Dole ne a yi rajistar mafarauta a ƙarƙashin ingantattun dokoki, tare da bayyanannun jagora kan nau’in da aka halatta farauta.
“Ana iya farautar namun daji ne kawai don dalilai na halal, kuma dole ne a rubuta dukkan kashe-kashen kuma a gudanar da bincike a hukumance,” in ji Sawaba.
Ya bayyana damuwarsa kan yadda ake yin asarar namun daji a Kano sakamakon yadda ake zama a cikin birane, da farauta ba tare da ka’ida ba, da kuma rashin isasshen matakan da gwamnati ta dauka a kan kiyayewa, kulawa da tsare-tsare.
Ya ce don magance wadannan matsaloli, gwamnati ta himmatu wajen inganta lambun dabbobin na Kano, da nufin sanya shi a matsayin babban gidan namun daji a Najeriya domin jawo hankalin yawon bude ido da zuba jari.
Sawaba ya kuma bayyana cewa gwamnati na samar da wani babban tsari na shekaru takwas na kare namun daji.
Ya kara da cewa, cikakken shirin wanda masu ruwa da tsaki da masana suka hada, an tsara shi ne domin jagorantar ayyukan kiyayewa a jihar.
Yankin Lagos na yunƙurin mallake Arewacin Nijeriya: Kwankwaso
Sanata Rabiu Kwankwaso ya zargi gwamnatin Tarayyar Nijeriya da ƙoƙarin durƙusar da harkokin kasuwanci a Arewacin ƙasar ta hanyar fito da sabuwar dokar haraji.
Tsohon gwamnan Kano kuma ɗan takarar shugaban Nijeriya na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi zargin cewa yankin Lagos yana yunƙuri “mai ƙarfi na mallake” Arewacin Nijeriya.
Jagoran na jam’iyyar NNPP, ya yi wannan zargi ne a Kano ranar Lahadi lokacin bikin yaye ɗaliban Jami’ar Skyline da ke birnin na Kano.
Duk da yake bai ambaci sunayen mutanen yankin na Lagos da yake zargi suna neman yi wa Arewacin ƙasar mulkin mallaka ba, sai dai wasu na gani yana magana ne game da shugaban Nijeriya Bola Tinubu wanda tsohon gwamnan Lagos ne kuma babban mai faɗa a ji a yankin Kudu Maso Yammacin Nijeriya.
Kwankwaso ya ce: “Akwai yunƙuri mai ƙarfi daga Yankin Lagos na mallake wannan ɓangare [ Arewaci] na Nijeriya.”
Kwankwaso ya gargadi ma’aurata su guji duba wayoyin juna
Tsohon gwamnan na jihar Kano ya ce hakan ne ya sa wasu mutanen yankin na Lagos suka tsoma baki a harkokin masarautar jihar Kano inda suka hana gwamnatin jihar zaɓen sarkinta.
“A yanzu, Lagos ta hana mu zaɓen Sarkinmu shi ya sa Lagos ta shigo har tsakiyar Kano ta saka nata sarkin,” in ji Kwankwaso.
Kazalika jagoran na jam’iyyar NNPP ya zargi gwamnatin tarayyar Nijeriya da yunƙurin durƙusar da harkokin kasuwanci a arewacin ƙasar ta hanyar fito da sabuwar dokar haraji.
Kawo yanzu dai babu wani martani a hukumance game da wannan zargi.