Gwamnatin Kano ta ba da gudummawar Motoci 78 na sintiri don bunkasa aikin Yan Sanda
Gamnatin jihar Kano ta baiwa rundunar ‘yan sandan jihar tallafin sabbin motocin sintiri guda 78. Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya mika motocin a hukumance a wani bikin da aka gudanar a gidan gwamnati a ranar Talata.
Sanarwar da Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ruwaito Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yaba wa kokarin ‘yan sandan na wanzar da zaman lafiya a Jihar, ya kuma yi alkawarin ci gaba da bayar da goyon bayan gwamnatinsa ga jami’an tsaro.
“Yayin da muka taru a nan, bari in tunatar da ku cewa babban nauyin da ke kan kowace gwamnati shi ne samar da tsaro,” in ji gwamnan. “Bayar da wadannan motocin sintiri guda 78 ga dukkan sassan ‘yan sanda a jihar Kano ya nuna aniyarmu ta tabbatar da tsaro da walwalar kasuwanci a jihar.”
Ya kuma mika godiyarsa ga sauran jami’an tsaro kan kokarin da suke yi na wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, inda ya bayyana hadin gwiwarsu a matsayin mai matukar amfani.