Gwamnatin jihar Sokoto ta kama wata budurwa don tayi kira kan matsalar tsaron garinsu
Gwamnatin jihar Sokoto ta kama wata budurwa don tayi kira ga Gwamnan jihar kan halin rashin tsaron da ya addabi garinsu a wani bidiyon da ya yita yawo na budurwar a kafofin sada zumunta inda budurwar take kiran sunan Gwamnan kai tsaye akan lamarin rashin tsaro.
Kafar AbbaPantami ta samu sahihin labarin cewa a jiya Lahadi da yamma Gwamnatin jihar ta tura aka kama budurwar inda a yau Litinin ta gabatar da ita a gaban kotu kan zargin yiwa Gwamnan jihar rashin kunya.
A yanzu haka budurwar tana tsare a hannun hukuma a jihar Sokoto, sunan budurwar Hamdiya Sidi dake karamar hukumar Wurno jihar Sokoto, garin nasu yana daya daga cikin yankunan dake fama da matsalolin rashin tsaro.