Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudirinta na magance matsalolin muhalli a jihar
Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudirinta na magance matsalolin muhalli a jihar ta hanyar hadin gwiwar da shiri na bankin duniya da gwamnatin tarayya mai keyi na (ACReSAL).
Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyara wajen aikin dinke wasu kwarurruka da ke da zaizayar kasa a Bulbula-Gayawa a karamar hukumar Ungoggo a karkashin shirin na ACRESAL.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’ar sadarwa ta Maryam Abdulqadir Kano-ACRESAL ta fitar.
Gwamna Yusuf ya tabbatar wa al’ummar Bulbula-Gayawa game da kammala duk wani shiri na fara gudanar da ayyukan gwamnati a wurin.
Gwamna Abba ya ce gwamnatin jihar ta dauki kwararan matakai na yaki da ayyukan kwasar yashi ba bisa ka’ida ba a yankuna da dama na jihar.