Gwamnatin Dikko Radda ta kulla yarjejeniyar haƙar ma’adinai ta biliyoyin naira 2024

Gwamnatin Dikko Radda ta rattaɓa hannu kan yarjejeniyar haƙar ma'adinai a faɗin jihar da kamfanin Geoscan na ƙasar Jamus.

Spread the love

Gwamnatin Dikko Radda ta rattaɓa hannu kan yarjejeniyar haƙar ma’adinai a faɗin jihar da kamfanin Geoscan na ƙasar Jamus.

Gwamnatin Dikko Radda ta kulla yarjejeniyar haƙar ma'adinai ta biliyoyin naira 2024
Dikko Radda

BBC hausa ta rawaito cewa, Shugaban hukumar haƙar ma’dinai ta jihar Katsina, Umar Abbas Dangi ne ya bayyana haka yayin rattaɓa hannu kan yarjejeniyar tare da wakilan kamfanin Geoscan a Berlin.

Abbas wanda ya wakilci gwamna Dikko Radda, ya ce yarjejeniyar za ta taimaka wajen samarwa jihar kuɗaɗen shiga da kuma ayyukan yi.

Ya ƙara da cewa ganin kwarewar Geoscan wajen aikin haƙar ma’adinai a Najeriya, ya janyo suka kulla yarjejeniyar, inji Dikko Radda.

“Kamfanin ya kware wajen haƙar ma’adinai yadda ya dace ba tare da yin wani mummunan tasiri kan muhalli ba,” in ji Umar Dangi.

Sun yaba wa gwamna Dikko Radda da wannan yunkuri da ya yi wajen ganin ɗorewa da kuma bunƙasar ɓangaren haƙar ma’adinai. Inji Dikko Radda.

Dikko Radda, Dikko Radda

YANZU-YANZU: Gwamna Dikko ya kaddamar da sabbin jami’an tsaron cikin gida kashi na biyu domin kawo karshen matsalar tsaro a Katsina

YANZU-YANZU: Gwamna Dikko ya kaddamar da sabbin jami’an tsaron cikin gida kashi na biyu domin kawo karshen matsalar tsaro a Katsina
Tsaro

Gwamnatin Jihar Katsina ta Ƙaddamar da Jami’an Tsaron Cikin Gida (Community Watch Corps) Rukuni na II

A ranar Juma’a 8 ga watan Nuwamba 2024, Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD, CON, ya ƙaddamar da Rukuni na II na jami’an tsaron cikin gida (Cwatch) guda 550 da suka fito daga kananan hukumomi goma da ke maƙwabtaka da ƙananan hukumomin da yan ta’adda suka fi addaba.

A jawabin buɗe taron Kwamishinan tsaron cikin gida Dr. Nasir Mu’azu, ya bayyana yau muna ƙaddamar da jami’an tsaron cikin gida rukuni na biyu wannan ya biyo bayan ƙoƙarin mai girma gwamna na ganin cewa an kawo ƙarshen ta’addanci a jihar Katsina.

Jami’an tsaron kuma mun ɗauko su ne daga ƙananan hukumomi goma da suke maƙwabtaka da ƙananan hukumomin da muka ɗauko rukunin farko wanda anan ne matsalar tafi ta’azzara.

Ƙananan hukumomin da suka fito sun haɗa da Funtua, Malumfashi, Ɗanja, Bakori, Musawa, Matazu, Charanchi, Batagarawa Kurfi, da Dutsin-ma, ya kuma bayyana jami’an sun samu horo ta tare da dabarun yaƙi fiye da wanda aka baiwa na baya.

A jawabin shi gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD, CON, ya bayyana wannan rana a matsayin rana mai muhimmanci a jihar Katsina da kuma tarihin wannan gwamnatin tashi, sabo da rana ce da zamu sake ƙaddamar da rukuni na biyu na jami’an tsaron cikin gida.

Shekarar da ta gabata munyi nasarar samun sa’a a cikin wannan yaƙin da muke da yan fashin daji duba da yanda wancen rukunin na jami’an mu haɗin guiwa da jami’an tsaro suka daƙile hare-hare da dama a faɗin jihar Katsina, wanda hakan yaba manoman mu damar yin aikin gona cikin kwanciyar hankali sabo da kaso chasa’in da biyar na gonakin Katsina an noma su a bana.

Duk a cikin hanyoyin da muke bi wajen daƙile matsalar nan mun samar da alawus ga sama da mutum 6,000 da suka haɗa da masu unguwanni, limamai, da kuma ladanai, domin sune ke cikin al’umma kuma sune zasu iya taimakawa jami’an tsaron namu wajen gudanar da ayyukan su ta hanyar shawarwari da kuma bayanan sirri.

Daga ƙarshe ina kira gare ku da ku nuna halin ɗa’a a lokacin gudanar da ayyukan ku kuma kuyi aiki tuƙuru domin ganin mun ceto jihar mu daga wannan hali da take ciki kuma kowanen ku ba zai tafi gida ba tare da ya amshi dukkan wasu kayan aiki da suka dace ba ga Babura da motocin da muka tanadar maku nan.

Insha Allah kuma ina da tabbacin zamu kawo ƙarshen wannan matsalar a jihar Katsina.

Wanda suka halarci wurin akwai Mataimakin gwamnan jihar Katsina Hon. Faruk Lawal Joɓe, Kakakin majalisar dokokin jihar Katsina Rt.Hon Nasiru Yahya Daura, Shugaban ma’aikatan gidan gwamnati Hon. Jabiru Abdullahi Tsauri, Sakataren Gwamnan Hon. Abdullahi Aliyu Turaji, yan majalisar Dokoki, yan majalisar zartarwa da sauran su.

 

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da dalibai 13 da suke cin zarafin  abokan karatunsu a jahar Enugu

Gamnatin tarayya ta bayar da umarnin dakatar da wasu dalibai 13 da ake zargin suna da hannu a cin zarafi da aka yi wa ’yan uwansu da ke makarantar sakandare (SS1) a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Enugu na tsawon makonni shida a ranar 7 ga Nuwamba.

Ministan Ilimi Dr. Maruf Alausa ya bayar da umarnin dakatarwar ne domin share fagen gudanar da cikakken bincike kan lamarin da kwamitin ladabtarwa da ma’aikatar ilimi ta tarayya ta kafa.

Umurnin ya biyo bayan yada wani faifan bidiyo mai tada hankali a shafukan sada zumunta, inda aka ga wasu gungun dalibai suna cin zarafin wani dalibin da aka gano cewa dalibin SS1 ne.

Darektan yada labarai da hulda da jama’a a ma’aikatar, Folasade Boriowo, a cikin wata sanarwa a ranar Laraba a Abuja, ta ce Dakta Alausa ya sake jaddada aniyar ma’aikatar wajen ganin an samar da ingantaccen yanayi na koyo a dukkan makarantun tarayya a fadin Najeriya.

Ya kuma tabbatar wa iyaye da masu riko da kuma sauran jama’a cewa za a yi duk abin da ya dace don dawo da zaman lafiya da kuma tabbatar da tsaron daliban FGC Enugu.

“Wani rahoto na baya-bayan nan da ma’aikatar ilimi ta tarayya ta samu ya yi nuni da irin yadda ake cin zarafi a Kwalejin Gwamnatin Tarayya (FGC), Enugu, wanda ya haifar da damuwa sosai game da tsaro da kuma da’a a cikin makarantun.

‘Yan sandan Najeriya sun kashe mutum 24 a zanga-zangar tsadar rayuwa ta watan Agusta – Amnesty

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta ce binciken da ta yi kan yadda hukumomin Najeriya, suka murkushe zanga-zangar kin jinin gwamnati a watan Agusta, ya nuna cewa jami’an kasar sun kashe akalla masu zanga-zangar 24 tare da tsare wasu fiye da 1,200.

VOA tace, Rahoton mai shafuka 34 da Amnesty International ta fitar a ranar Alhamis, ya samo asali ne daga shaidun gani da ido da hirarraki da ma’aikatan lafiya da iyalai da abokan wadanda abin ya shafa.

Amnesty ta ce ‘yan sandan Najeriya sun yi amfani da karfin tuwo kan masu zanga-zangar da suka taru domin nuna adawa da tsadar rayuwa.

Ta ce ‘yan sanda sun kashe akalla mutane 24, ciki har da yara biyu. An samu asarar rayuka a fadin jihohin Borno da Kaduna da Kano da Katsina da Jigawa da kuma Neja.

A cewar rahoton, ‘yan sanda sun yi ta harbe-harbe kai tsaye a kusa da kan wadanda lamarin ya rutsa da su, yayin da wasu da abin ya shafa suka shaki hayaki mai sa hawaye.

Isa Sanusi, darektan kungiyar Amnesty a Najeriya, ya yi imanin cewa adadin wadanda suka mutu na iya karuwa sosai.

“Ko a yau da muke kaddamar da wannan rahoto a Kano, iyalai da dama sun fito suna shaida mana cewa ‘ya’yansu sun bace, wasu da dama kuma ana kyautata zaton an kashe su ko kuma ana tsare da su a asirce, don haka batun gaba daya ya fi yadda ake tsare da su. Wannan kawai ya nuna cewa hukumomin Najeriya ba su shirya amincewa da cewa jama’a na da ‘yancin yin zanga-zangar lumana ba.”

Zanga-zangar da aka yi a watan Agusta, wadda masu shirya ta suka kira “Ranaku Goma na Fushi”, ta kasance mayar da martani ne ga tsadar rayuwa da mutane da dama suka yi imani da cewa sauye-sauyen da Shugaba Bola Tinubu ya yi ne ya haifar da su, ciki har da cire tallafin man fetur.

Hukumomin ‘yan sandan Najeriya ba su mayar da martani kan zargin Amnesty ba, amma a baya sun musanta yin amfani da harsashi mai rai wajen dakile zanga-zangar.

Kakakin ‘yan sandan kasar bai amsa kiran da Muryar Amurka ta yi masa ba.

A cikin watan Oktobar 2020, zaluncin ‘yan sanda ya haifar da zanga-zangar adawa da Rundunar ‘yan sandan SARS.

Zanga-zangar dai ta kawo karshe ne sakamakon harbi da bindiga da aka yi a kofar karbar harajin Lekki da ke Legas.

Najeriya dai ta dade tana fama da ta’asar ‘yan sanda, duk kuwa da alkawuran da aka sha yi mata na cewa za ta kara kaimi.

 

YANZU-YANZU: Gwamna Dikko Radda ya kaddamar da sabbin jami’an tsaron cikin gida kashi na biyu domin kawo karshen matsalar tsaro a Katsina

Gwamnatin Dikko Radda ya Ƙaddamar da Jami’an Tsaron Cikin Gida (Community Watch Corps) Rukuni na II

A ranar Juma’a 8 ga watan Nuwamba 2024, Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Radda PhD, CON, ya ƙaddamar da Rukuni na II na jami’an tsaron cikin gida (Cwatch) guda 550 da suka fito daga kananan hukumomi goma da ke maƙwabtaka da ƙananan hukumomin da yan ta’adda suka fi addaba.

A jawabin buɗe taron Kwamishinan tsaron cikin gida Dr. Nasir Mu’azu, ya bayyana yau muna ƙaddamar da jami’an tsaron cikin gida rukuni na biyu wannan ya biyo bayan ƙoƙarin mai girma gwamna Dikko Radda na ganin cewa an kawo ƙarshen ta’addanci a jihar Katsina.

Jami’an tsaron kuma mun ɗauko su ne daga ƙananan hukumomi goma da suke maƙwabtaka da ƙananan hukumomin da muka ɗauko rukunin farko wanda anan ne matsalar tafi ta’azzara.

Ƙananan hukumomin da suka fito sun haɗa da Funtua, Malumfashi, Ɗanja, Bakori, Musawa, Matazu, Charanchi, Batagarawa Kurfi, da Dutsin-ma, ya kuma bayyana jami’an sun samu horo ta tare da dabarun yaƙi fiye da wanda aka baiwa na baya.

A jawabin shi gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Radda PhD, CON, ya bayyana wannan rana a matsayin rana mai muhimmanci a jihar Katsina da kuma tarihin wannan gwamnatin tashi, sabo da rana ce da zamu sake ƙaddamar da rukuni na biyu na jami’an tsaron cikin gida, inji Dikko Radda.

Shekarar da ta gabata munyi nasarar samun sa’a a cikin wannan yaƙin da muke da yan fashin daji duba da yanda wancen rukunin na jami’an mu haɗin guiwa da jami’an tsaro suka daƙile hare-hare da dama a faɗin jihar Katsina, wanda hakan yaba manoman mu damar yin aikin gona cikin kwanciyar hankali sabo da kaso chasa’in da biyar na gonakin Katsina an noma su a bana, inji Dikko Radda.

Duk a cikin hanyoyin da muke bi wajen daƙile matsalar nan mun samar da alawus ga sama da mutum 6,000 da suka haɗa da masu unguwanni, limamai, da kuma ladanai, domin sune ke cikin al’umma kuma sune zasu iya taimakawa jami’an tsaron namu wajen gudanar da ayyukan su ta hanyar shawarwari da kuma bayanan sirri.

Daga ƙarshe ina kira gare ku da ku nuna halin ɗa’a a lokacin gudanar da ayyukan ku kuma kuyi aiki tuƙuru domin ganin mun ceto jihar mu daga wannan hali da take ciki kuma kowanen ku ba zai tafi gida ba tare da ya amshi dukkan wasu kayan aiki da suka dace ba ga Babura da motocin da muka tanadar maku nan.

Insha Allah kuma ina da tabbacin zamu kawo ƙarshen wannan matsalar a jihar Katsina.

Wanda suka halarci wurin akwai Mataimakin gwamnan jihar Katsina Hon. Faruk Lawal Joɓe, Kakakin majalisar dokokin jihar Katsina Rt.Hon Nasiru Yahya Daura, Shugaban ma’aikatan gidan gwamnati Hon. Jabiru Abdullahi Tsauri, Sakataren Gwamnan Hon. Abdullahi Aliyu Turaji, yan majalisar Dokoki, yan majalisar zartarwa da sauran su.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button