Gwamnan jihar Legas, Sanwo-Olu, ya amince da sakin fursunoni 55 a fadin jihar.
Wata sanarwa da kwamishinan shari’a na jihar, Lawal Pedro, SAN ya sanya wa hannu, ta ce an ba da umarnin a gaggauta sakin fursunoni 40 yayin da sauran kuma za a sake su bayan kammala wa’adin watanni uku zuwa shida.
Pedro ya bayyana cewa amincewar sakin fursunonin na karkashin ikon da Gwamna ke dashi a sashe na 212 (1) cikin baka da (2) cikin baka na kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya na shekarar 1999.
Ya kuma kara da cewa matakin ya kuma yi daidai da alkawarin da gwamnan ya yi na rage cinkoso a gidajen gyaran hali a Legas a wani bangare na sake fasalin bangaren shari’a a jihar.
A cewarsa, majalisar ba da shawara kan sassaucin ta yi nazari kan tuhume tuhumen da ake wa fursunonin kafin daukar matakin sakin nasu.