Gwamnan Ekiti ya nada sabon alkalin kotun jihar.

Gwamnan jihar Ekiti, Mista Biodun Oyebanji, ya nada Mai shari’a Lekan Adekanye Ogunmoye a matsayin mukaddashin babban alkalin jihar.

Spread the love

Gwamnan ya yi wannan nadin ne La’akari da karfin ikon da sashe na 271 (4) na kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 ya bai wa Gwamna (kamar yadda aka yi wa kwaskwarima).

Nadin mai shari’a Ogunmoye zai fara aiki ne daga ranar 5 ga Nuwamba, 2024.

Mai shari’ar Ya maye gurbin tsohon babban alkalin kotun, Hon Justice John Oyewole Adeyeye, wanda ya mutu a ranar 4 ga Nuwamba, 2024.

An haife shi a ranar 6 ga Nuwamba, 1963, kuma an nada shi alkali a ranar 1 ga Afrilu, 2010 kafin ya zama babban alkalin alkalan.

Mista Yinka Oyebode, mai ba Gwamnan shawara na musamman kan harkokin yada labarai, ya ce Oyebanji ya yi wa sabon mukaddashin alkalin alkalai fatan alheri da kuma fara aiki lafiya.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button