Gwamnan Bauchi ya jaddada kudurin inganta lafiya a Jahar
jihar
Gwamnan jihar Bauchiq, Bala Mohammed, ya jaddada kudirin gwamnatinsa na hada hannu da masu hannu da shuni na kasa da kasa domin bunkasa harkokin kiwon lafiya a jihar.
Ya yi wannan alkawarin ne a jiya a yayin wata ziyarar ban girma da jami’an kungiyar likitocin ta Médecins Sans Frontières (Doctors Without Borders) suka kai musu, karkashin jagorancin shugaban ma’aikata kuma daraktan kasa, Dr. Adams Usmane Ngare.
Mohammed ya nuna godiya ga ayyukan da kungiyar ta Médecins Sans Frontières ke yi kuma ya jaddada cewa kiwon lafiya ya kasance fifiko ga gwamnatinsa.
Yayin da yake lura da cewa gudummawar da kungiyar ta bayar ya inganta harkar kiwon lafiya a jihar Bauchi, Mohammed ya yi alkawarin tabbatar da biyan kudaden takwarorinsu domin saukaka wa jihar damar samun shirye-shiryen bayar da tallafi na kasa da kasa.
A jewar jaridar leadership Gwamna Bala Mohammed ya kuma yabawa kungiyar likitocin ta Médecins Sans Frontières kan ayyukan jin kai da suke yi a Najeriya da ma duniya baki daya, sannan ya kara jaddada aniyar gwamnatinsa na tallafawa ayyukansu a jihar.
A nasa bangaren, shugaban manufa kuma darakta na kasa, Dokta Adams Usmane Ngare, ya bayyana irin rawar da kungiyar ke takawa a matsayin kungiyar kula da harkokin jin kai ta kasa da kasa da ta mai da hankali kan tallafawa lafiyar yara, shirye-shiryen abinci mai gina jiki, da yaki da cututtuka masu barazana ga rayuwa.
Labarai Masu Alaka
Farashin man fetur na iya raguwa bayan da matatar mai ta Fatakwal ta dawo aiki
Ya amince da gudummawar da kungiyar likitocin ta Médecins Sans Frontières ke yi a jihar Bauchi, wadanda suka hada da inganta tsarin asibitoci da samar da kayan aikin lafiya.
Daraktan na kasa ya yabawa gwamna Bala Mohammed bisa goyon baya da hadin gwiwa da kungiyar tare da bada tabbacin ci gaba da hadin gwiwarsu domin inganta harkokin kiwon lafiya a jihar.