Gwamnan Abba Kabir na jihar Kano zai kori kwamashinonin da suka ga za

Spread the love

Gomnan jihar Kano a arewacin Najeriya ya bayyana aniyarsa ta sauke duk wani kwamashinan sa da aka gano ba shi da himma a aikin sa nan gaba kaɗan.

Wata sanarwa da mai magana da yawunsa Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi rahoton kwamatin da ke duba ƙwazon kwamashinonin.

Nan gaba kaɗan al’umma za su ji matakin da gwamnatin za ta ɗauka, in ji sanarwar.

Ya ƙara da cewa gwamnan ya ce rahoton ma ba zai yi wani amfani ba yanzu saboda tsawon shekara ɗaya da rabi da ya yi yana aiki tare da su ya ba shi damar gane himmarsu ciki da baya, saboda haka da kansa zai yanke hukuncin.

Yanzu haka dai jam’iyyar NNPP mai mulki a Kanon na fama da rikici, musamman a ɓangaren ƙungiyar Kwankwasiyya da tsohon Gwamna Rabiu Kwankwaso ke jagoranta, inda wasu jiga-jigai suka ce sun fita daga cikinta.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button