Gwamna Zulum na Borno ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu saboda Kirsimeti

Gwamnan ya bayar da umarnin ne domin sauƙaƙa wa waɗanda ba asalin ‘yan ba zuwa garuruwansu.

Spread the love

Gwamna Zulum ya bayar da umarnin ne domin sauƙaƙa wa waɗanda ba asalin ‘yan ba zuwa garuruwansu.

Gwamna Zulum na Borno ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu saboda Kirsimeti
Gwamna Zulum

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bai wa mutum 710 waɗanda ba ’yan asalin jihar ba, tallafin sufuri domin su koma garuruwansu don yin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara tare da ’yan uwansu. Trust radio.

An ƙaddamar da wannan shiri ne a tashar Borno Express a ranar Asabar, inda aka fara jigilar mutum 285 zuwa wurare daban-daban a faɗin Najeriya.

Za a ci gaba da wannan jigilar, inda za a sake tashin mutum 285 a ranar Lahadi, yayin da sauran za su bar Maiduguri a ranar Litinin, inji Zulum.

Da yake magana yayin ƙaddamar da shirin, shugaban ƙungiyar Ohaneze All Progressives Congress (APC), Cif Ugochukwu Egwidike, ya bayyana cewa kowane daga cikin matafiya 710 zai karɓi tallafin sufuri kyauta tare da kuɗi Naira 50,000, inji Zulum.

Haka kuma, mata kimanin 250 da mazansu suka rasu kuma ba za su iya tafiya ba, an tanadar musu da Naira 50,000 kowacce domin gudanar da bikin Kirsimeti, inji Gwamna Zulum.

Cif Egwidike, ya yaba jajircewar Zulum wajen tallafa wa mabuƙata, ya ce shirin zai rage raɗaɗin talauci tare da walwalar al’umma.

Ya ƙara da cewa gwamnatin Zulum tana ɗaukar nauyin Kiristoci zuwa Kudu domin gudanar da ibada, baya ga tallafin sufuri kyauta da ake bai wa waɗanda ba ’yan asalin jihar ba a lokacin bukukuwan Kirsimeti.

“Bugu da ƙari, gwamna Zulum ya taimaka wa waɗanda iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa, ciki har da waɗanda ba ’yan asalin jihar ba.

’Wannan yana nuna irin adalcin gwamna Zulum wajen tallafa wa dukkanin jama’a ba tare da la’akari da ƙabila ko addini ba.”

Shi ma Sarkin Yarbawa a Jihar Borno, Alhaji Hassan Alao Yusuf, ya yaba wa gwamnan bisa wannan karamcin.

Ya ce tsarin safarar mutane da ba ‘yan asalin jihar ba alama ce ta yadda gwamna Zulum ke gudanar da ayyukan alheri ga al’umma.

Mamban kwamitin amintattu na Ohanaeze Ndigbo, Pharm Napoleon Egbonu, ya bayyana cewa irin wannan taimako daga gwamna Zulum abin koyi ne ga sauran shugabanni.

Ya ce, “Karamcin Gwamna Zulum zai taimaka wajen tabbatar da haɗin kai da amana tsakanin al’umma a faɗin ƙasar nan.”

Hakazalika, Babban Manajan Kamfanin Sufuri na Borno Express, Grema Zanna, ya yaba wa gwamna Zulum bisa wannan taimako.

Ya bayyana cewa shirin sufuri kyauta na daga cikin dabarun gwamna Zulum na rage matsalolin sufuri da tsadar kayan masarufi ga mazauna jihar.

Zulum, Zulum, Zulum, Zulum, Zulum, Zulum, Zulum, Zulum, Zulum, Zulum.

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025
Gwamna Abba Kabir

Gwamnatin ta ce za ta gurfanar da waɗanda ba sa biyan haraji a gaban kotu.

Gwamnatin Jihar Kano, ta ce tana fatan samun sama da Naira biliyan 20 a kowane wata uku na shekarar 2025, wanda zai kai jimillar sama da Naira biliyan 80 a shekarar.

Haka kuma, gwamnatin ta sanar da shirin gurfanar da waɗanda suka ki biyan haraji a gaban kotu, a wani yunkuri na inganta tsarin karɓar haraji a jihar.

Shugaban Hukumar Karɓar Haraji ta Jihar Kano (KIRS), Dokts Zaid Abubakar ne, ya bayyana hakan yayin gabatar da bayani a wani taron bita na manyan jami’an gwamnatin jihar.

Kakakin gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne, ya tabbatar da hakan.

Dokts Abubakar, ya ce waɗannan sauye-sauyen ba wai don ƙara yawa. haraji ba ne, na da kuma nufin inganta yadda ake tattara haraji da kuma tabbatar da cewa kowa yana biyan haƙƙinsa.

Ya kuma bayyana cewa, hukumar ta samu gagarumar nasara a ƙarshen 2024 bayan gwamna ya sauke tsohon shugaban hukumar tare da naɗa sabbin shugabanni.

Don samun ƙarin kuɗaɗen shiga a 2025, gwamnan na shirin ƙaddamar da sabon tsarin karɓar haraji a jihar.

Wannan tsarin yana da nufin samar da ƙarin kuɗaɗen shiga, wanda zai bai wa gwamnatin damar cika alƙawuranta a ɓangaren ilimi, lafiya, da inganta ababen more rayuwa.

Ko kasafin kudin shugaba Tinubu zai iya farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya?

Ko kasafin kudin shugaba Tinubu zai iya farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya?
Kasafin kudi

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi wa kasafin kuɗi na 2025 da ya gabatar a gaban majalisar dokokin ƙasar ranar Laraba take da Farfaɗowa domin tabbatar da zaman lafiya, da gina rayuwar ‘yan kasa.

Tinubu ya gabatar da kasafin na naira tiriliyan 47.9, wanda yafi na shekarar da ta gabata da kashi 36.8 cikin 100. Kasafin shine na biyu da Tinubu ya yi tun bayan rantsar da shi a matsayin shugaban kasar a watan Mayun 2023.

An dai ɗora kasafin kuɗin na 2025 ne a kan dala 75 a kan kowacce gangar ɗanyen mai guda kuma ana sa ran Najeriyar za ta samar da gangar ɗanyen man fiye da miliyan biyu duk rana a shekarar mai kamawa.

Shugaba Bola Tinubu ya shaida wa majalisun dokokin cewa suna fatan samun naira tiriliyan 34.82 ta hanyar kuɗin shiga domin zuba wa a kasafin.

Sai dai kuma ya ce kasafin na da giɓin naira tiriliyan 13.08 wato kashi 3.08 cikin 100 na jimillar kasafin, yayin da ake hasashen gwamnatin za ta ciyo bashin tiriliyan 13 a cikin gida da waje domin cike giɓin.

A cikin jawabinsa, shugaba Tinubu ya ce tattalin arziƙin Najeriya ya samu haɓaka da kashi 3.46 cikin 100 a kaso na uku cikin huɗu na shekarar 2024, fiye da 2.54 a irin wannan lokacin a 2023.

Ya ƙara da cewa asusun Najeriya a ƙasar waje yanzu ya kai kusan dala biliyan 42, wanda ya samar da kariya daga duk wata komaɗar tattalin arziƙi da ka iya tasowa.

Sai dai masana tattalin arziƙi a Najeriya na ganin babu wani tabbas ko kasafin kudin zai iya farfado da tatattalin arziƙin ƙasar kamar yadda gwamnatin ta Tinubu ke so ‘yan ƙasa su amince.

Kasancewar tattalin arziƙin Najeriya na cikin rashin lafiya, yana kuma samun koma-baya a kowane lokaci, in ji Dr Murtala Abdullahi Ƙwara masanin tatattalin arziƙi na Jami’ar Umaru Musa Ƴar’adua da ke jihar Katsina.

Ya ƙara da cewa da wuya kasafin kudin na 2025 ya iya farfado da tattalin arziƙin Najeriya. Idan aka kalli alƙalumman da ake da su a ƙasa za a iya cewa da kamar wuya.

Wasu alƙaluman da aka sanya cikinsa abu, da yawansu ba haka suke ba a harkar tatattalin arziƙi ta zahiri. Farashin dala da kuma yadda ake sayar da mai a yanzu da kuma adadin man da ake iya haƙowa a yanzu, duka hasashe ne kawai.

Dr. Ƙwara ya ce hasashen da aka yi cikin kasafin kuɗi kan canjin dalar Amurka kan N1,400, zai yi wahala a iya samun haka saboda idan aka yi la’akari da farashin da yanzu dalar take kai, kuma ba ta fara yin ƙasa ba duk da cewa an kusa shiga shekarar.

Ko me zai faru idan aka kasa cim ma hasashen da aka yi?

Abin da zai faru shi ne, za a iya rasa damar aiwatar da kasafin kuɗin, wato duk abin da aka ce za a yi da kasafin kuɗin ba za a yi ba har sai an sake nemo hanyar da za a cike giɓin, ko da ta hanyar ciwo bashi ne, a cewar Dr. Ƙwara.

Masanin ya ce Najeriya ta jima cikin ƙangin bashi. Amma ya ce ba kowane bashi ne yake zama illa ba, yana mai cewa ya danganta da yadda aka yi amfanin da kudin da aka ciyo bashin.

To mece ce matsalar Najeriya game da bashin?

Matsalar Najeriya ita ce, ba a yin abin da ya dace da kudin da ake amsowa idan aka yi la’akari da ƙididdigar da ake da ita. Misali, me ya sa za ka ciwo bashi saboda saya wa ƴan majalisa motoci ko kuma wasu abubuwa?

Yadda majalisar dokoki a jihar Zamfara ta dakatar da ƴaƴanta na tsawon shekara 1 daga aiki

Yadda majalisar dokoki a jihar Zamfara ta dakatar da ƴaƴanta na tsawon shekara 1 daga aiki
Zauren majalisar Zamfara

Ana ci gaba da samun rashin fahimta game da batun mayar da wasu ƴan majalisar dokokin jihar Zamfara kan kujerunsu, bayan da majalisar ta dakatar da su kusan shekara guda da ta gabata.

Yanzu haka wasu daga cikinsu ma sun fara tunanin sauka daga mukamin na su, don a sake gudanar da zaben cike gurbi a yankunan mu ta yadda jama’arsu za su samu wakilci tun da duk wani kokari na ganin an warware matsalar bai kai ga gaci ba.

BBC Hausa ta ruwaito cewa a ranar 27 ga watan Fabrairu ne majalisar dokokin jihar ta Zamfara ta dakatar da wadannan yan majalisa 8 bisa zarginsu da gudanar da zaman majalisar ba bisa ka’ida ba.

Ƴan majalisar takwas su ne Bashir Aliyu (PDP-Gummi 1) Amiru Keta (PDP-Tsafe Ta Yamma) Nasiru Abdullahi (PDP-Maru Ta Kudu) Bashir Masama (PDP-Bukkuyum Ta Arewa) Faruku Dosara (APC-Maradun 1) Ibrahim Tukur (Mazabar APC-Bakura) Shamsudeen Hassan (APC Talata-Mafara Ta Arewa) da kuma Bashiru Sarkin-Zango (PDP-Bungudu Ta Yamma).

Ɗaya daga cikinsu Honarabul Ibrahim Tudu Tukur, ya faɗawa BBC Hausa cewa ”Matsalolin tsaro ne da suka ta’azzara ne suka sa muka je muka buɗe majalisa muka zauna muka yi kira ga gwamnatin jiha da ta tarayya da su dauki matakin gaggawa don magance wannan matsala, wannan shine abun da ya ɓata masu rai”

Ya ƙara da cewa majalisar malamai da majalisar masarautu da shi kansa shugaban PDP na jihar da wasu jagorori kamar tsohon gwamnan jihar Abdulaziz Yari sun yi kokarin sasanta lamarin, amma dukka basu yi nasara ba.

To sai dai a nasa martanin mai magana da yawun majalisar dokokin jihar ta Zamfara Hamisu Alhaji Faro, ya ce suma suna na su kokarin domin ganin an sasanta wannan al’amari, amma abun da ke kawo cikas shine su ƴan majalisar da aka dakatar sun ki amincewa abun da suka yi kuskure ne ballantana su ba da hakuri a yafe masu.

”Sun karya dokoki na kundin tsarin mulki, suma sun san haka, kuma an gaya masu muna so a yafewa juna, amma su zo su ba wa shugabanni hakuri musamman shi kakakin majalisa, amma suka ce Wallahi tallahi baza su yi hakan ba”

Wasu daga cikin yan majalisar da aka dakatar dai na zargin gwamnan jihar Dauda Lawal da hannu a dakatar da su kasancewarsu yan jam’iyyar APC ne, sai dai kuma a cikinsu akwai hatta ƴan jam’iyyar gwamnan ta PDP.

Wannan al’amari dai ya sa kananan hukumomin yan majalisar sun rasa wakilci a majalisar dokokin jihar tsawon shekara guda, wani abu da ya sa masu sharhi ke ganin zai haifarwa mazaɓun na su gagarumar asara, saboda rashin waklcin da zai rika kai kokensu gaba.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button