Gwamna Mutfwang ya amince da mafi karancin albashi na naira 70,000 ga ma’aikatan Filato

Spread the love

Gwamnan jihar Plateau, Barista Caleb Mutfwang ya amince da fara aiwatar da mafi karancin albashi na N70,000 ga ma’aikata a jihar nan take.

Amincewar ya biyo bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar da kwamitin ya yi kan daidaita albashin a ranar Laraba 13 ga Nuwamba, 2024.

A wata sanarwa da shugaban ma’aikatan jihar Stephen Gadong ya fitar, ya ce aiwatar da sabon albashin ya nuna kudirin gwamnati na ba da fifikon jin dadin ma’aikatanta wajen amincewa da gagarumar rawar da suke takawa wajen ciyar da manufofin ci gaban gwamnati.

Gadong ya karfafa gwiwar ma’aikatan gwamnati da su rungumi wannan karimcin ta hanyar sake jajircewa wajen gudanar da ayyukansu tare da sabunta kwazo da himma wajen bunkasa al’adun samarwa da nagarta a hidimar jihar.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button