Gomnatin tarayya tana son haɓaka Wutar Lantarki na Sa’o’i 20 Kullum nan da 2027.

Spread the love

Gwamnatin tarayya ta ce tana ci gaba da shirye-shiryen tabbatar da masu amfani da wutar lantarki a Najeriya na tsawon sa’o’i 20 a kullum nan da shekarar 2027.

Da take jawabi a taron makon makamashi a birnin Cape Town na kasar Afirka ta Kudu, mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin makamashi, Olu Verheijen, ta yi bayani kan isashshen zuba jari a bangaren man fetur da iskar gas na Najeriya.

Sanarwar da Daraktan yada labarai na fadar shugaban kasa, Abiodun Oladunjoye, ya fitar a ranar Alhamis, ta ruwaito Verheijen na cewa nan da zuwa shekarar 2027, Najeriya na da burin tabbatar da samar da wutar lantarki na sa’o’i 20 a kullum ga masu amfani da shi a birane da cibiyoyin masana’antu.

Verheijen ta bayyana shirin da gwamnatin Bola Tinubu ke jagoranta na samar da ingantacciyar hanyar samar da wutar lantarki ga ‘yan Najeriya miliyan 86 a halin yanzu, inda ya kara da cewa shirin na da nufin inganta tabbatar da kudaden shiga.

Kalaman na ta na zuwa ne a daidai lokacin da ake yawan rugujewar tsarin samar da wutar lantarki a Najeriya, lamarin da ya janyo katsewar wutar lantarki a fadin kasar.

Tsaunukan samar da wutar sun ruguje ne a ranar Alhamis, lamarin da ya zama na biyu a wannan makon kuma karo na goma sha biyu a cikin watanni goma sha daya da suka gabata.

A halin da ake ciki kuma, gwamnatin tarayya ta hannun hukumar wayar da kan jama’a ta kasa (NOA), ta danganta yawaitar rugujewar wutar lantarkin na kasa wanda ke haifar da katsewar wutar lantarki a fadin kasar sakamakon gazawar kamfanonin rarraba wutar lantarkin (DisCos) da su ka yi amfani da wutar lantarki.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button