Gobara ta lashe kasuwar Jos jihar Filato

Spread the love

Wata gobara ta lalata kadarori na miliyoyin naira a kasuwar Laranto da ke karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato.

 

Daily trust ta ruwaito cewa an sha samun barkewar gobara a kasuwar. A shekarar da ta gabata wani sashe na kasuwar ya kone kurmus sakamakon matsalar wutar lantarki, lamarin da ya yi sanadiyar lalata kayayyaki da suka hada da ababan hawa.

 

Wakilinmu ya tattaro cewa sabon lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na daren ranar Lahadi bayan da aka rufe harkokin kasuwanci a ranar.

 

An tattaro cewa mutane sun garzaya kasuwa da daddare domin taimakawa wajen kashe gobarar.

 

Shugaban kasuwar Alhaji Idris Shehu ya shaida wa Aminiya cewa gobarar ta lakume kayyakin miliyoyin naira, inda ya ce har yanzu ba a san musabbabin faruwar lamarin ba.

 

Ya ce, “Kusan sassa uku na kasuwar da suka hada da katako, kayan sawa na hannu da kuma kayan daki sun sami matsala sosai. Duk da cewa ba za mu iya tantance ainihin adadin kudaden da aka yi asarar ba a halin yanzu, amma tsananin barnar na nuni da cewa mun yi asarar miliyoyin naira.”

 

Da yake tsokaci kan lamarin, shugaban sashen katako na kasuwar, Umar Aliyu, ya koka da cewa da a ce jami’an kashe gobara sun isa kan lokaci, da an rage asarar da ake yi.

 

Ya ce, “Ba da jimawa ba da aka sanar da mu lamarin, mun ziyarci ofishin kashe gobara na garin, muka kai rahoton lamarin. Sai dai jami’an ofishin sun koka da cewa basu da man dizal da zai iya sarrafa motocinsu.

 

“Duk da kokarin da muka yi na shawo kan su, sun ki amsa, saboda karancin man dizal. Sai da Shugaban Jos ta Arewa da Kwamishinan Albarkatun Ruwa suka je suka kirawo ma’aikatan kashe gobara daga gidan gwamnati, inda a karshe suka kashe gobarar. Idan ba don tsoma bakinsu ba, da lamarin ya fi muni,” ya kara da cewa.

 

 

Obasanjo ya yi kira da a sauke shugaban INEC

 

Tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya yi kira da a yi garambawul na gaba ɗaya ga tsarin zaɓen ƙasar.

 

Da yake jawabi a taron Chinua Achebe Leadership Forum, Jami’ar Yale, a Amurka, Obasanjo ya yi kira musamman da a tsige Mahmood Yakubu, Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), da sauran jami’ai a duk matakai.

 

A lokacin da yake bayyana zaɓen 2023 a matsayin “abun kunya,” Obasanjo ya jaddada muhimmancin sake fasalin tsarin zaɓen domin dawo da sahihanci da amincewa.

 

Haka nan, tsohon shugaban ya ba da shawarar a rage tsawon wa’adin shugabannin INEC da kuma aiwatar da cikakken bincike kafin a naɗa mutane, domin hana naɗin waɗanda ke da ra’ayin ɓangaranci.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button