Gawuna ya fi dacewa a bai wa muƙamin minista — Gwarzo
Tsohon Ministan Ma’aikatar Gidaje da Raya Birane, Abdullahi Gwarzo, ya ce ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen 2023, Nasiru Yusuf Gawuna, ya fi dacewa a bai wa muƙamin minista maimakon Yusuf Ata.
Gwarzo, ya ce kamata ya yi a bai wa ɗan takarar gwamnan Kano a zaɓen 2023, Nasiru Yusuf Gawuna matsayin nasa maimakon bai wa Yusuf Ata.
Idan an ware wannan muƙami ne don Kano ta Tsakiya ne, to Gawuna wanda ya yi takarar gwamna a 2023 wanda yake shugabanta a Kano ta Tsakiya, shi ya kamata a fara tunani.
Gawuna ya kamata a bai wa wannan muƙamin. Idan ya ƙi ya karɓa, sai a duba wani. Wasu ’yan takarar gwamna daga Filato da Zamfara sun samu manyan muƙamai, in ji Gwarzo.
Gwarzo ya bayyana haka ne cikin wata hira da Sashen Hausa na BBC, wanda ya ce ya yi mamakin tsige shi da aka yi, domin bai yi wani abu ba da ya saɓa wa doka ko kuma gazawa a aikinsa ba.
Ya ce, Na yi mamaki saboda ba a same ni da laifin gazawa ko aikata wani abu ba da ya saɓa wa doka. Ni dai ƙaramin minista ne, yayin da babban ministan ke kula da yawancin ayyukan ma’aikatar.
Kafin a tsige ni, Shugaban ya shaida min cewa ya ɗauki wannan matakin ne saboda akwai ‘yan siyasa da dama daga Kano ta Arewa.
Mun bayar da shawarwari, amma ba a ɗauke su ba. Daga nan na fara tunanin cewa akwai wasu mutane da suka shigo tsakani don ɗaukar wannan mataki, domin a ganina wannan ba hujja ba ce mai ƙarfi.
Wasu dai tunanin rikici ya danno kaina jam’iyyar APC a Jihar Kano, wanda hakan ne ya sa wasu suka yi uwa suka yi makarɓiya wajen tsige Gwarzo daga muƙamin minista.