Kamfanonin rarraba wutar lantarki sun kara farashin mita daga N117k zuwa N149k
Masu amfani da wutar lantarki sun yi ta korafi a kafafen sada zumunta na zamani game da karin farashin kudin mita da kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) suka yi a kasar.
Idan dai ba a manta ba a kwanakin baya ne Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki a Najeriya sun sanar da karin farashin wutar lantarki daban-daban, wanda hakan ya zama karin farashin na biyu cikin watanni hudu.
A cewar DisCos, farashin mita mai hawa daya ya tashi daga kusan N117,000 zuwa N149,800.
Wannan adadin ya nuna an samu karuwar kashi 28.03 bisa dari ko kuma N32,800, ya danganta da kamfanin rarraba mitocin.