Dillalan mai za su koma sayen man fetur daga matatar Dangote.

Bayan shafe makwanni ana tattaunawa, kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya IPMAN, ta bayyana a ranar Litinin cewa ta cimma yarjejeniya da matatar Dangote domin mambobinta su sayo man fetur daga matatar.

Spread the love

Shugaban kungiyar dillalan na kasa, Abubakar Maigandi Shettima, ya shaidawa manema labarai a Abuja cewa yarjejeniyar ta kuma shafi daukar man fetur da man dizal da kananzir kai tsaye.

Shettima ya yi kira ga ‘yan kasuwa da su tallafawa matatar, yana mai jaddada cewa irin wannan tallafin zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

A baya dai ‘yan kasuwar man da suka hada da wasu ‘yan kungiyar IPMAN sun dage kan shigo da mai domin yin gogayya da kayayyakin da matatar Dangote ke samarwa.

Shettima ya bayyana irin nasarorin da aka samu a tattaunawar da aka yi a baya-bayan nan, inda ya ce: “Bayan ganawar da muka yi da Alhaji Aliko Dangote da wasu manyan ma’aikatansa a Legas, muna farin cikin sanar da mu cewa:

“Ma’aikatar matatar man Dangote ta amince da baiwa kungiyar dillalan damar dakon mai kai-tsaye da dizel da kuma kalanzir domin kaiwa ma’ajiyar kungiyar da yan kasuwa.

“Wannan sabon tsari da matatar man Dangote zai tabbatar da samar da kayayyakin PMS a duk fadin Najeriya a kan farashi mai rahusa ga ‘yan Najeriya.

“Ya kamata dukkan ‘yan kungiyar su ba da cikakken goyon baya ga matatar man ta Dangote, domin wannan hanya ce da ta dace, idan aka yi la’akari da dimbin alfanun da ke tattare da hada-hadar koma-baya da kuma tasirinta na dogon lokaci a kasuwannin canji na Najeriya.

“Ya kamata ‘yan kungiyar IPMAN a fadin kasar nan su dogara da matatun man Dangote da matatun man Najeriya wajen wanda hakan zai kara samar da guraben ayyukan yi a Najeriya da kuma yin daidai da ajandar sabunta bege na Shugaba Bola Tinubu.

Har ila yau, Shettima ya yi magana game da yunkurin Gwamnatin Tarayya na karfafa amfani da motocin iskar Gas (CNG) a matsayin madadin masu amfani da fetur.

Ya ce: “Game da CNG, ina kira ga daukacin membobinmu na IPMAN da su fara shirye-shiryen sauyawa zuwa gidajen mai na iskar gas.

“Ko shakka babu CNG na da damar sake farfado da tattalin arzikinmu da inganta rayuwar ‘yan Najeriya. IPMAN ta himmatu sosai wajen tallafawa wannan shiri.

“Muna kuma kira da a hada kai da Gwamnatin Tarayya domin a gaggauta samun nasarar shirin CNG a Najeriya.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button