DA DUMI-DUMI: Tankar mai ta sake fashewa a Jigawa
Wata tanka mai dauke da man fetur ta fashe a jihar Jigawa dake arewa maso yammacin Najeriya, lamarin da ya tsorita jama’ar dake kan iyaka da Jigawa da Kano.
Lamarin ya faru ne a ranar Talata, 12 ga watan Nuwamba, 2024, a kusa da kauyen Gamoji, kan hanyar Kano zuwa Maiduguri. Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya (FFS) a Jihar Jigawa, Aliyu M.A, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
A cewar Aliyu, “da misalin karfe 10:43 na safe ne muka samu kiran gaggawa daga Zubairu Ahmad, Hakimin Kuho, inda ya sanar da mu wani hatsarin da wata tanka ta yi a Tsaida, Kwanar Kalle, kusa da kauyen Gamoji.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, wannan shi ne karo na biyu da fashewar tankar dakon mai a yankin cikin wata guda. A ranar 15 ga Oktoba, 2024, makamancin haka ta faru a garin Majia da ke karamar hukumar Taura, inda wata motar dakon mai da ta taso daga jihar Kano zuwa Nguru ta jihar Yobe ta tarwatse, inda ta kashe mutane sama da 170.
3 Comments