Cire tallafin man fetur zai kawo karshen cin hanci da rashawa tsawon shekaru 10 – Sen Musa
Shugaban kwamitin majalisar dattijai mai kula da harkokin kudi, Sanata Sani Musa, ya tabbatar da cewa cire tallafin man fetur ya kawo karshen cin hanci da rashawa na tsawon shekaru da dama.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya, Musa ya bayyana cewa an yi kuskure fahimtar kalaman da ya yi a baya game da batun cire tallafin da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi.
Da yake bayyana matsayin sa game da cire tallafin da kuma cewa sadaukar da kai wajen magance matsalolin ‘yan kasa, Musa ya nuna jin dadinsa da yadda jama’a suka shiga tare da nuna damuwar su kan kalaman sa na farko game da cire tallafin.
Duk da haka, zan so in fayyace matsayata, domin kamar an yi wa magana ta mummunar fassara, in ji Musa.
Lokacin da na ayyana, ‘Cire tallafin shine mafi kyawun abin da ya faru da Najeriya,’ ban yi niyyar raina kalubalen tattalin arzikin ’yan kasa ba. Maimakon haka, hujjata ta samo asali ne daga gaskiyar cewa, tsawon shekaru, biyan tallafin ya wadata wasu zaɓaɓɓu a cikin kuɗin ƙasa.
Daruruwan biliyoyin nairori, wadanda ya kamata a sanya hannun jari a muhimman ababen more rayuwa, ilimi, da kiwon lafiya, maimakon haka sun amfana da wasu tsiraru masu gata, tare da hana sama da ‘yan Najeriya miliyan 230 muhimman albarkatu da damammaki.
Cire tallafin wani muhimmin mataki ne na kawar da cin hanci da rashawa da kuma samar da albarkatun a inda ake bukata da gaske, in ji shi.
Musa ya yarda cewa dole ne a dauki kwararan matakai na tallafawa wannan sauyin don rage tsanani da talakawan Najeriya ke yi.
Wannan ya haɗa da dabarun saka hannun jari a cikin shirye-shiryen jin daɗin jama’a, samar da tsaro, da tallafi don haɓakar tattalin arziƙi a kowane mataki, wanda shine babban abin da na fi mayar da hankali a kai.