Cire tallafin man fetur ya kawo karshen haramtaciyyar kasuwancin ‘yan fasa-kwauri – Nuhu Ribadu
Mai bawa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Mal. Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa cire tallafin man fetur da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi ya kawo karshen fasa-kwaurin da ake yi a fadin kasar nan domin ‘yan Najeriya kalilan ne ke cin gajiyar wannan manufa.
Ribadu ya bayyana haka ne a ranar Laraba a Abuja, a wajen taron kwanturola janar na hukumar Kwastam da aka gudanar a Abuja, inda ya kara da cewa Najeriya na tallafawa kasashe makwabta ne kawai sakamakon fasa-kwaurin da ake yi a kan iyakokin kasar.
Ni dan yankin kan iyaka ne kuma a kullum ina yawan samun kiraye-kirayen yadda hukumar Kwastam ke wahalar da masu fasa-kwauri. Abin mamaki mutanen da ke taimaka musu sun hada da sojoji amma yanzu komai ya kasance a baya domin duk wadannan janar-janar da jami’an tsaron da ke taimaka masu fasa-kwaurin mai an dauke su aka maye gurbinsu da wata sabuwar tawaga.
Haka nan tallafin da dukkan mu ke magana a kai wanda ya durkusar da kamfanin na NNPC yana yi wa kasashe makwabta ne kawai ba ma ‘yan Najeriya ba. Muna ba da tallafi ga Nijar, Chadi, Burkina Faso, Kamaru, Jamhuriyar Benin, Ghana da kuma ’yan Najeriya masu wayo da suka kira kansu ‘yan kasuwar man fetur, in ji shi.
Najeriya ce kasa daya tilo a duniya da kowa ya zama dan kasuwan mai saboda tallafin. Kuna iya kirga kusan gidajen mai guda 100 daga Abuja zuwa Kaduna kadai. Sai dai jindadin da muka ba su ya kare, haka nan kuma harkar safarar man fetur ta kan iyaka ta kare, ya kara da cewa.
Ya ci gaba da bayyana cewa, shirye-shiryen da hukumar kwastam ta yi a baya-bayan nan, musamman ma Operation Whirlwind na dakile fasa kwauri ya haifar da gagarumin sakamako a cikin sauran kokarin.
Tun da farko a nasa jawabin, Kwanturolan Hukumar Kwastam ta Najeriya, Bashir Adeniyi, ya bayyana cewa hukumar ta cimma burinta na samar da kudaden shiga na shekarar 2024 na Naira Tiriliyan 5.07.
A cewarsa, ya zuwa ranar 12 ga watan Nuwamba, 2024, hukumar ta samu nasarar karbo naira tiriliyan 5.07.
Ya kara da cewa, yayin da ya rage sama da wata guda a karshen wannan shekarar, an kiyasta cewa Ma’aikatar za ta zarce kaso 10 cikin 100 na kudaden shiga.
Ina mai farin cikin sanar da cewa, a jiya 12 ga Nuwamba, 2024, da misalin karfe 13:10, Hukumar Kwastam ta Najeriya ta cimma burinta na samun kudin shiga na shekarar 2024 na Naira Tiriliyan 5.07, inda ta tara NGN 5,079,455,088,194.38, yayin da ya rage fiye da wata guda a cikin kasafin kudi.
Wannan aikin na musamman da aka yi hasashen zai wuce abin da muka sa a gaba da kashi 10 cikin 100 yana tabbatar da tsarin hadin gwiwarmu na tattara kudaden shiga da saukaka kasuwanci, in ji shi.
Adeniyi ya kara da cewa, a wani bangare na kokarin inganta iya aiki, hukumar ta kammala shirye-shiryen kafa jami’an Kwastam.