Bambamci tsakanin ƴan camama da ƴan sentimental
Tasirin kafofin sadarwa na zamani, musamman TikTok da Instagram ya sa matasan arewa da dama sun zama masu shirye-shiryen barkwanci, inda wasunsu suke shiryawa su gyara sannan su fitar da shi da wayoyinsu kawai, wanda hakan ya sa wasu ke cewa camama ce ta dawo.
BBC Hausa ta ruwaito cewar A tsakanin shekarar 1998 zuwa 2000, masana’antar Kannywood ta haifar da wasu ɓangarori biyu: camama da sentimental, inda duk da cewa akwai an yi tsama a tsakaninsu, sun nishaɗantar da masu kallo, musamman a arewacin Najeriya.
Fina-finan chamama an fi shirya su ne a ƙauyuka, sannan ba a kashe kuɗi sosai wajen shiryawa.
A ɗaya ɓangaren kuma, fina-finan sentimental suna samun tsari fiye da na camama, sannan fina-finan soyayya sun fi yawa.
Daga cikin jaruman camama da suka yi shuhura akwai Rabilu Musa Ibro da wadda ke yawan fitowa a matsayin matarsa wato Tsigai da Ƙulu da Yautai da Malam Dare da Daushe da Bosho.
Haka kuma akwai ƴan wasan barkwanci na zamani, waɗanda suke yi suna ɗorawa a shafukansu na sada zumunta mutane suna dariya suna nishaɗantuwa.
Asalin chamama da sentimental
Malam Ibrahim Sheme, masani kan harkokin fina-finan Hausa ya ce camama ɓangaren fina-finan Hausa ne na barkwanci, wanda ake yi a gurguje, shi kuma sentimental fina-finan da aka fi tsarawa kuma ake ɗaukar lokaci.
“Camama su ne fina-finai na barkwanci na su Ibro da Tsigai da Ƙulu da Yautai da sauransu. Ba zan iya bayyana rana kaza da aka fara amfani da kalmar ba, amma tunda aka fara fim ɗin Hausa ake yin fina-finan camama. Suna nufin fina-finan da ake yinsu a gurguje da kuɗin kaɗan,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, “sentimental kuma fina-finai ne da suka fi inganci, sun fi bin ƙa’idojin shirya fim kuma ana ɗaukar lokaci mai tsawo ana yi sama da na camama,” in ji Sheme.
Shi ma Dokta Muhsin Ibrahim, malami a jami’ar Cologne da ke Jamus ya ce a iya bincikensa, bai gano daidai lokacin da aka fara amfani da kalmomin biyu ba, sannan ya ƙara da cewa ba a Kannywood kaɗai ake samun irin waɗannan rabe-raben ba, “har Hollywood ta Amurka ana samun haka.”
Sai dai ya ƙara da cewa a lokacin da marigayi Rabilu Musa Ibro yake ganiyarsa, fina-finan camama, duk da cewa da kuɗi kaɗan aka shirya su, wasunsu suna fin na sentimental tashe da samar da kuɗin.
Shi ma fitaccen ɗan camama, Rabiu Daushe ya ce a tsakaninsu ne suka ƙirƙira sunayen biyu.
“Su ƴan ɓangaren sentimental masu fina-finan soyayya da ƙyale-ƙyale ne, sai suke ganin kamar masu yin fim ɗin barkwanci a cikin ƙazanta suke yi. Wannan ya sa suka fara kiransu ƴan camama, inda suka iyakance cewa da ƙanƙanin kuɗi kaɗan za ka haɗa fim ka gama.”
Ya ƙara da cewa suma ƴan camamar sun mayar da martani, inda “suke ganin ai masu fim ɗin soyayya suna waƙoƙi suna kawo ɓata musu aiki, wato za su jawo musu zagi. Shi ne a lokacin su Ibro da Ƙulu da Yautai idan suna fim sai suke cewa ‘waɗancan ƴan sentimental ne’. Wato santi da mental ta hauka. Su kuma ƴan sentimental idan ƴan camama sun yi wanu abu, sai su riƙa cewa, ‘ƴan camama ne fa.’
An daina camama a Kannywood?
A baya-baya, musamman lokacin da marigayi yake ganiyarsa, an yi wani zama da zaman takiya ya tsananta a tsakanin ƴan camama da ƴan sentimental a masana’antar ta Kannywood, inda suka riƙa caccakar juna.
Daushe ya ce a lokacin ne “za ka ji ƴan sentimental suna cewa fim ɗin camama ne fa kawai, nawa suka kashe. Yaya za ka haɗa fim ɗinsu da mu. Akwai wani fim ina gani sunansa Ba’asi, inda a ciki suka yi wata waƙa suna cewa ‘camama ce ta samu yanzuuu, ke ko kina ta noke-nokeee, amarya.”
Daushe ya ƙara da cewa shi ma Ibro a fim ɗin ‘Ibro Ɗanƙwairo’ an yi wata waƙa cewa, “Mu yanzu kau sai camama, kasuwa nan take kawo riba.”
Sai dai Daushe ya ce ba daina camama aka yi ba, domin “A yanzu idan ka hau tiktok kafin ka ga abubuwa da suka yaɗu na soyayya biyar, za ka camama 50. Ai duk masu wasan barkwanci ƴan camama ne wato waɗanda suka shirya dirama cikin ƴan mintuna ƙadan kuma mutum ya kalla ya nishaɗantu.”
Daushe ya ce ba za a taɓa daina camama ba, “saboda duk duniya ana yi, kuma za ka ana yi a wasu harsunnan daban, amma kuma ka kalla ka yi dariya. Don haka da shi aka fara buɗe shafin fim, kuma idan ma za a daina, to shi ne ƙarshe.”
Daushe ya tabbatar da tsamar da aka yi tsakanin ɓangarorin biyu, “akwai lokacin da aka haɗa fim tsakanin jagororin ɓangarorin biyu domin a samu sulhu, amma bayan fim ɗin sai abubuwa suka ƙara rincaɓewa. Amma daga baya mun samu maslaha cikin ikon Allah komai ya wuce ya zama labari.”
A game da koma-baya da aka samu a fina-finan camama, Dr Muhsin ya ce cigaba ne ya zo.
A cewarsa, “Rasuwar Ibro ce ta jawo koma-bayan ɓangaren duk da cewa tun kafin rasu ma ya yi fina-finai na camamama a birni irin su Ƙarangiya da Maja da Hajiya babba da sauransu.”
Muhsin ya ƙara da cewa cigaba ne ya kawo haka, “misali Carmen McCain ta faɗa min cewa lokacin da aka yi fim ɗin ‘Ibro ya auri Baturiya’ ba ta san da fim ɗin ba, kawai ta je wani bincike ne, sai aka ce ga Baturiya, sai aka shirya fim ɗin a nan take.”