Bai ka mata Matasan Nijeriya su ke ficewa daga kasar ba – Fashola

Spread the love

Babatunde Fashola, tsohon ministan wutar lantarki, ayyuka da gidaje, ya bukaci matasan Najeriya da su daina ficewa daga kasar zuwa kasashen waje, duk da kalubalen tattalin arziki da kasar ake fuskanta.

Da yake jawabi a wajen wani taro karo na 8 da na 9 na jami’ar Elizade da ke jihar Ondo, Fashola ya jaddada muhimmancin jajircewa, inda yace da yawa daga cikin manyan mutane irin su Folorunso Alakija da Cif Tunde Afolabi, sun fuskanci irin wannan wahalhalu amma sun zabi tsayawa su ba da gudunmawa wajen ci gaban kasa.

Michael Ade-Ojo, wanda ya kafa Jami’ar Elizade, ya bayyana gamsuwa da ci gaban da cibiyar ke samu wajen samar da wadanda suka kammala karatun digiri a duniya. Duk da karancin kudaden gudanarwar jami’ar

Mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Kayode Ijadunola ya tabbatar da cewa jami’ar Elizade ta himmatu wajen taimakawa daliban da suka kammala karatunsu wadanda za su iya kawo sauyi a tattalin arziki da fasaha na kasar nan, inda ya bayyana kokarin da makarantar ke yi na inganta bincike da hada kan al’umma.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button