Badenoch ta mayarwa da Shettima martani kan kiran da ya yi mata da ta cire sunan Nijeriya a jerin sunayen ta
Badenoch ta mayarwa da Shettima martani
Kemi Badenoch, shugabar jam’iyyar Conservative Party, ta Birtaniya kuma haifaffiyar ƙasar, ta mayarwa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima martani kan kiran da ya yi mata na ta cire sunan Nijeriya a jerin sunayen ta.
A wata ziyara da ta kai Amurka, Badenoch ta bayyana Najeriya a matsayin “ƙasa da kusan komai ya lalace.”
Ta kara da cewa akwai rashin zaman lafiya da cin hanci da rashawa a Najeriya, lamarin da ya sa mataimakin shugaban kasar ya bayyana kalaman nata a matsayin rashin mutuntawa.
Labarai Masu Alaka
Yan Najeriya 10,000 ake tsare da su bisa laifukan shige da fice a 2024 – Shettima
Shettima ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya yi a wani taro a Abuja, inda ya ce me zai hana Badenoch din ta cire Kemi daga sunanta idan har ba ta yi alfahari da ‘kasarta ta asali.”
Amma a martanin da mai magana da yawun Badenoch ya mayar wa mataimakin shugaban kasar ta ce ta “ta na nan kan bakar ta” kuma ta jaddada cewa “ba ita ce kakakin gwamnatin Najeriya ba.”
VANGUARD NEWS“Ta na jagorantar ƴan adawa kuma ta na alfahari da rawar da ta ke takawa a kasar nan; gaskiya ta fada, kuma tana gabatar da abubuwa yadda su ke kuma ba za ta janye maganarta ba,” kamar yadda ta shaida wa manema labarai.