Badakalar N1.3tn: Har yanzu Okowa na hannun EFCC.

Har yanzu dai tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa yana tsare a ofishin hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC a Fatakwal, jihar Ribas.

Spread the love

Hakan ke nuni da cewa ya zama dare na biyu a hannun hukumar yaki da cin hanci da rashawa.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar APC reshen jihar Delta ta goyi bayan tsare tsohon gwamnan, inda ta bayyana hakan a matsayin wani mataki da ya dace a yakin da Najeriya ke yi da cin hanci da rashawa.

Okowa, wanda ya kasance mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, a ranar Litinin, ya kai rahoto a ofishin EFCC, biyo bayan gayyatar da masu bincike suka yi masa kan karkatar da N1.3trn.

Majiyoyi sun ce ana zargin shi da kin bayar da asusun ajiyar kudaden da kuma wani N40bn da ake zargin ya yi ikirarin cewa ya mallaki hannun jari a UTM Floating Liquefied Natural Gas.

“An kuma yi zargin cewa ya sayi hannun jarin N40bn a daya daga cikin manyan bankunan kasar nan, wanda ke nuna kashi takwas cikin dari. An dai yi zargin an yi amfani da kudaden ne don wasu dalilai.

“Masu bincike suna kuma binciken karkatar da kudaden da tsohon gwamnan ya yi don mallakar gidaje a Abuja da Asaba a jihar Delta.”

Sai dai wata majiya mai tushe ta shaida wa Jaridar Punch a ranar Talata cewa har yanzu ba a saki tsohon gwamnan ba saboda yawan zargin da ake yi masa.

Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC reshen Jihar Delta, Valentine Onojeghuo, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya bukaci Hukumar EFCC da ta ci gaba da binciken yadda wasu tsofaffin gwamnoni da jami’an gwamnati ke gudanar da harkokin kudi.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button