Babu wata zanga-zanga da za ta iya hana mu tsaftace birnin tarayya Abuja – Wike
Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya sha alwashin cewa babu wata zanga-zanga da za ta iya hana yunkurin tsaftace babban birnin kasar.
Aminiya ta ruwaito cewa, a makon da ya gabata ne rundunar da ke aiki da umarnin ministan ta rusa matsugunin Ruga da ke kan titin filin jirgin sama na Lugbe, lamarin da ya harzuka jama’a.
Masu zanga-zangar karkashin jagorancin wani dan fafutuka, Deji Adeyanju, sun mamaye kan tituna yayin da suke zargin rundunar tsaro da aka fi sani da “Operation Sweep”, sun na yunkurin hana su.
Sai dai da yake magana a lokacin da ya ziyarci matsugunin da aka rusa, da yammacin Lahadi, Ministan, wanda ya samu rakiyar manyan hafsoshin tsaro a yankin, ya ce ya je wurin ne domin shaida abinda ya faru a yankin.
Da yake jawabi ga wadanda lamarin ya faru da su, Ministan ya ce babu gudu babu ja da baya a shirin da yake na tsaftace birnin tarayyar.
Sai dai ya bukaci kakakin wadanda abin ya shafa da su turo da wakilansu biyar zuwa Sakatariyar birnin tarayya domin tattaunawa kan abin da za a yi musu.
Tun da farko mai magana da yawun wadanda abin ya shafa Abba Garu ya shaidawa ministan cewa sun shafe shekaru 35 suna zaune a yankin.
Ya ce kimanin mutane 10,000 ne wannan aikin ya shafa tare da lalata dukiyoyinsu da kasuwancinsu.
Ya kuma roki ministan da ya samar musu da wani mazuguni da zasu zauna.