Babu wata baraka tsakanin Kwankwaso da Abba ~ Gwamnatin Kano
Gwamnatin jihar Kano ta yi watsi da rade-radin cewa an shata layi tsakanin Engr. Abba Kabir Yusuf da Tsohon Gwamna Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso.
Wannan dai na zuwa ne bayan da ake ta yaɗa labarin cewa Gwamnan ya daina ɗaukar wayar uban gidan nasa, a daidai lokacin da wasu jiga-jigan jam’iyyar suka bar tafiyar Kwankwasiyya a jiya Lahadi.
Malam Salisu Yahaya Hotoro shi ne Babban Mai Taimakawa Gwamnan Kano kan harkokin kafafen sada zumunta, ya yiwa Freedom Radio karin bayani a kai.