Babu ruwanmu da abin da ke faruwa a Syria – Trump 2024
Lokacin da Donald Trump tare da sauran shugabannin ƙasashen duniya suka je birnin Paris a makon da ya gabata domin ganin yadda aka sake buɗe ginin coci mai tarihi na Notre Dame Cathedral, ƴan tawayen Syria na kan hanyarsu ta zuwa Damascus domin karɓe mulki daga hannun shugaba Bashar al-Assad.
Lokacin da Donald Trump tare da sauran shugabannin ƙasashen duniya suka je birnin Paris a makon da ya gabata domin ganin yadda aka sake buɗe ginin coci mai tarihi na Notre Dame Cathedral, ƴan tawayen Syria na kan hanyarsu ta zuwa Damascus domin karɓe mulki daga hannun shugaba Bashar al-Assad.
A wannan lokaci hankalin shugabanni, ciki har da Trump na bibiyar abubuwan da ke faruwa a ƙasar ta Syria.
Ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa: “Syria ta zama shirme, amma ba abokanmu ba ne. Kamar yadda BBC ta rawaito.
Ya ƙara da cewa “BAI KAMATA AMURKA TA YI WANI ABU A KAI BA. WANNAN BA FAƊANMU BA NE. A BAR SU SU YI KAYANSU. KADA A TSOMA BAKI!”
Waɗannan abubuwa da zaɓaɓɓen shugaban na Amurka ya wallafa tamkar tunatarwa ce game da ƙudurinsa na tsame hannu daga cikin al’amuran ƙasashen ƙetare.
Sai dai hakan ya kuma jefa ayar tambaya kan irin abubuwan da za su faru a gaba. Ganin yadda yaƙin na Syria ya shafi yankuna da dama na duniya da hannun da shugabannin ƙasashen duniya da dama a ciki, zai iya yiwuwa a ce Trump ya ce “babu ruwan shi” da Syria a wannan lokaci da aka kawar da gwamnatin Bashar al-Assad?
Ko Trump zai janye sojojin Amurka daga ƙasar?
Shin manufofin Trump sun yi hannun-riga da na shugaban Biden ne, kuma idan haka ne mene ne amfanin duk wani mataki mai muhimmanci da Biden zai ɗauka daga nan zuwa ƴan makonnin da suka rage kafin Trump ya kama mulki?
Gwamantin Amurka mai ci a yanzu na ta karakaina kan wasu jerin tattaunawa na diflomasiyya bayan abin da ya faru na rushewar gwamnatin Assad da kuma karɓe ikon da ƙungiyar HTS ta yi – ƙungiyar da Amurka ta ayyana a matsayin ta ƴan ta’adda.
Yanzu haka sakataren harkokin waje na Amurka, Antony Blinken na zirga-zirga tsakanin ƙasashen Jordan da Turkiyya domin ganin cewa ƙasashen Larabawa da kuma na Musulmi sun goyi bayan wasu sharuɗɗa da Amurka ke son kafawa game da makomar Syria.
Amurka ta ce dole ne Syria ta riƙa bayani kan duk matakan da take ɗauka kuma kada ta zama “sansanin ta’addanci”, kada ta yi barazana ga maƙwaftanta sannan kuma dole ne ƙasar ta lalata duk wasu makaman sinadarai masu guba da take da su.
Amma a ra’ayin Mike Waltz, mutumin da Donald Trump ya zaɓa a matsayin mai ba shi shawara kan tsaro, wanda ba a riga an tabbatar masa da muƙamin ba, yana dogaro ne da wani abu guda ɗaya idan aka zo maganar alaƙar Amurka da sauran ƙasashen duniya.
A wata tattaunawa da kafar talabijin ta Fox News cikin wannan mako, Waltz ya ce “an zaɓi Donald Trump da gagarumin rinjaye ne bisa alƙawarin cewa Amurka ba ta cusa kanta cikin ƙarin wasu yaƙe-yaƙe a Gabas ta tsakiya ba.”
Ya ce abubuwan kawai da Amurka ke da “ra’ayi sosai a kai” su ne ƙungiyar IS da kuma “ƙawayenmu na yankin Gulf”.
Bayanan Waltz tamkar bayani ne a taƙaice kan ra’ayin Trump game da Syria, wadda wani ɓangare ne na turakun rikice-rikicen da ake fama da su a Gabas ta tsakiya.
https://abbapantami.com/biden-da-trump-sun-sha-alwashin-mi%c6%99a-mulki-ba-tare-da-matsala-ba/
Zaɓabɓen shugaban Amurka Donald Trump da daɗaɗɗen abokin hamayyarsa a siyasance, shugaba Joe Biden sun gana a fadar White House a karon farko tun bayan fitar sakamakon zaɓen shugaban ƙasar, inda dukkanninsu su ka sha alwashin tabbatar da miƙa mulki a watan Janairu ba tare da wata matsala ba.
Shugabannin biyu sun zauna a kusa da juna a gaban garwashin wuta mai ruruwa a cikin ofishin shugaban ƙasa, wani yanayi da ke alamta kwanciyar hankali, amma ƙunshe da tankiya da ke tsakaninsu.
Biden ya marabci Trump da sake dawowa fadar White House, inda ya kuma taya shi murnar lashe zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana a ƙasar a kwanan nan, yana mai shan alwashin miƙa mulki ba tare da mishkila ba.
Biden mai shekaru 81 ya doke Trump a zaben shekarar 2020, amma kuma ya janye daga takarar shugaban ƙasa a wannan shekarar biyo bayan rashin kataɓus a muhawwarar ƴan takarar shugabancin ƙasa, ya kuma miƙa wa mataimakiyarsa, Kamala Harris takarar.
Ba a bai wa manema labarai damar yin ko da tambaya guda ba a yayin ganawar jagororin biyu, saboda an tura su waje duk da tambayoyin da su ka yi ta jefawa.