Ba ni da masaniya game da shirya taron addu’a na kasa – Remi Tinubu
Uwargidan shugaban kasar Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu ta ce ba ta shirya taron addu’a na kasa ba, kuma labaran da ake yadawa a wasu kafafen yada labarai na sada zumunta ba su da tushe balle makama.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Busola Kukoyi, mai magana da yawun uwargidan shugaban kasar Najeriya ya rabawa manaima labarai.
Sanarwar ta kara da cewa, uwargidan shugaban kasar ta yi imanin cewa addu’a abune da ya dace yan kasar suyi aduk inda suke.
Ta kuma yi imanin cewa yi wa Najeriya addu’a nauyi ne da ya rataya a wuyan kowane dan Najeriya, ba tare da la’akari da addini, siyasa, kabila ko harshe ba.
Ta shawarci jama’a da su rika tantance sahihancin duk wani labari da su ka ga ni a kafafen yada labarai.