Ana zargin yan daba da halaka wani dan sanda a jihar Adamawa
Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da kashe wani dan sanda mai suna Ibrahim Maizabuwa.
Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da kashe wani dan sanda mai suna Ibrahim Maizabuwa.
Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da kashe wani dan sanda mai suna Ibrahim Maizabuwa.
Wadanda ake zargin, Ezekiel Kefas mai shekaru 67 da Stephen Zabadi mai shekaru 44, sun fito ne daga gundumar Wamsa Suwa da ke karamar hukumar Lamurde ta jihar.
A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Suleiman Yahaya Nguroje, an kama wadanda ake zargin ne a ranar 19 ga Nuwamba, 2024.
A cewar jaridar Daily trust Nguroje ya bayyana cewa dan sandan da ya rasu, Danlami Ibrahim Maizabuwa ne ya kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda.
Bincike ya nuna cewa an kashe jami’in ne kuma aka binne shi a unguwar bayan ya ziyarci abokinsa Ezekiel Kefas.
A yayin da ake yi masa tambayoyi, an ruwaito Kefas ya yi ikirarin cewa wasu ’yan daba ne suka kashe jami’in bayan da ya yi zargin ya lalata dukiya tare da cin zarafin mutane a gidansa (Kefas).
Labarai masu alaƙa
“Abokina ya zo ya fara lalata dukiya da suka hada da tukunyar miya da ruwa a gidana tare da cin zarafin mutane a sakamakon haka mata da kananan yara suka yi ta hargitsi wanda ya jawo ‘yan daba suka yi masa duka har lahira.
“Wadanda suka kashe shi sun hada da Yakubu, Suleiman da Kilyobas. Suka yi masa duka da sanduna har ya mutu. Jiya, mun je gidajen waɗanda suka yi kisan, amma ba mu gamu da kowa a cikinsu ba,” inji Ezekiel yana cewa.
Kwamishinan ‘yan sanda, Morris Dankombo, ya bayar da umarnin gudanar da sahihin bincike kan lamarin tare da gurfanar da wadanda ake zargin.
Ƴansanda sun kama mutum 82 da ake zargi da aikata laifuka a Kano
Rundunar ‘Yansanda ta Jihar Kano ta kama mutum 82 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a cikin jihar daga ranar 1 ga Nuwamba zuwa 14 ga Nuwamba.
Wadanda aka kama sun hada da masu garkuwa da mutane, ‘yan fashi da makami, ‘yan daba, masu satar wayoyi, da masu safarar miyagun kwayoyi.
Da yake jawabi ga manema labarai a hedkwatar rundunar da ke Bompai, Kano, mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda, SP Abdullahi Kiyawa, ya ce an samu nasarar cafke wadannan mutane ne sakamakon dabarun yaki da laifuka da rundunar ta aiwatar.
“Aiwatar da wadannan dabaru ya haifar da sakamako mai kyau, inda aka samu nasarar ragargaza cibiyoyin laifuka kamar dakile ragowar ayyukan ‘yan daba a cikin birnin Kano.
“Sauran nasarorin sun hada da tarwatsa kungiyoyin ‘yan fashi da makami a kan iyakokin Jigawa-Kano da Bauchi-Kano, da kuma hana aukuwar garkuwa da mutane a kan iyakokin Kaduna-Kano da Katsina-Kano.”