Ana zargin jami’an NDLEA sun kashe wani ɗalibin sakandare a jihar Filato

Spread the love

Ana zargin cewa wasu jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) sun kashe wani ɗalibin sakandire a Unguwar Dangi ta Ƙaramar Hukumar Kanam da ke Jihar Filato.

Mazauna unguwar sun bayyana cewa jami’an sun kashe matashin mai suna Faisal Yakubu Hussaini yayin wani samame da suka kai yankin.

A cewar mazauna waɗanda suka nemi bahasin ko an kai samame yankin ne saboda aikata wani laifi, jami’an sun gaza bayar da wani gamsasshen bayani.

Shugaba da kuma Sakataren Ƙungiyar Ci gaban Kanam, Barista G Abdullahi da ND Shehu Kanam, sun tabbatar da faruwar lamarin yayin da suke Allah wadai.

Shugabannin sun bayyana damuwa kan lamarin da suka alaƙanta da ƙetare iyakar ’yancin matashin da abin ya shafa.

A yayin da suke tabbatar da cewa jami’an na NDLEA suna da damar aiwatar da ayyukansu bisa duk wani tanadi da doka ta yi, sun kuma yi tir da faruwar lamarin da cewa sai an bi wa matashin haƙƙinsa.

Cikin sanarwar da suka fitar, sun buƙaci mahukunta da su gaggauta kama jami’an da ake zargi da wannan aika-aikar domin su gurfana a gaban shari’a.

Kazalika, sun gargaɗi matasan yankin da su yayyafa wa zukata ruwan sanyi domin kiyaye doka da oda a yayin da suka cewa ba za su yi ƙasa a gwiwa ba don ganin an shari’a ta ɗauki matakin da ya dace.

Aminiya ta tuntubi mai magana da yawun rundunar NDLEA, Abba Muhammad Sani, inda ya ce zai gudanar da bincike gabanin mayar da martani kan lamarin.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button