Ana yi wa majalisar tarayya mummunar fahimta ne – Tajuddeen Abbas

Kakakin Majalisar Wakilai, Hon Tajuddeen Abbas, ya ce yawancin ‘yan Najeriya sun kasa fahimtar rawar da majalisar za ta taka a tsarin dimokuradiyya, yana mai jaddada cewa akwai bukatar a samar da ingantaccen ilimi kan Muhim manci majalisar tun da ga tushe.

Spread the love

Abbas ya bayyana haka ne a yayin babban taron muhawara tsakanin “majalisa da dimokuradiyya a 2024”, wanda Cibiyar Nazarin Majalisun dokoki da Dimokaradiyya ta kasa (NILDS) ta shirya a Abuja ranar Litinin.

 

Dan majalisar ya ce an yi taron ne domin baiwa matasan Najeriya damar gudanar da ayyukan majalisa da tsarin dimokuradiyya da suka hada da tsarin tabbatar da daidaito tsakanin bangarori uku na gwamnati.

 

Ya ce, “Abin takaici, sau da yawa ana samun rashin fahimta a tsakanin jama’a dangane da rawar da majalisa ke takawa. Wasu na ganin cewa majalisar wakilai ce kawai ta ’yan siyasa da ke zaune suna muhawara.

 

“Majalisa ita ce injin dimokuradiyya. Ita ce wurin da ake jin muryoyin jama’a da kuma yanke hukunci mafi muhimmanci da suka shafi al’umma. Domin dimokuradiyya ta yi aiki yadda ya kamata, dole ne ‘yan kasa su fahimci tsarinta da kuma rawar da kowace cibiya ke takawa.”

 

Ya roki matasan Najeriya da su jajirce wajen neman mukaman shugabanci ba wai a siyasa kadai ba, a kowane bangare na al’umma, “da sanin cewa muryar ku tana da muhimmanci kuma za ku iya kawo canji mai kyau.”

 

A jawabinsa na maraba, Darakta Janar na cibiyar nazarin, Farfesa Abubakar Suleiman, ya ce taron na da nufin samar da fahimtar juna, aiki da kuma aiwatar da dimokuradiyya a tsakanin daliban manyan makarantun sakandare a Najeriya.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button