Ana musayar wuta tsakanin sojoji da ƴan bindiga a Sokoto

Sojoji da mafarauta sun yi artabu da fitaccen ɗan bindiga, Bello Turji, a garin Gatawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.

Spread the love

Majiyoyi da dama daga Gatawa sun shaidawa wakilin Daily trust cewa an fara artabu da ‘yan bindiga da misalin karfe 6 na safe a yau.

Daya daga cikin majiyoyin da ta nemi a sakaya sunanta ta ce ‘yan bindigar sun yi yunkurin kai hari garin amma sojoji da mafarauta sun hana su shiga.

“Muna zargin Bello Turji ne da kansa yake jagorantar yakin. An fara musayar wuta da misalin karfe 6 na safe har zuwa wannan lokaci (2:45pm) da nake magana da ku, ana ci gaba da gwabzawa. Bangarorin biyu na ci gaba da musayar wuta.

“Muna cikin tsananin kaduwa domin babu wanda ya san abin da zai faru nan da ‘yan sa’o’i masu zuwa. Garin shiru; babu motsi. Babu mai shigowa ko fita daga garin a halin yanzu.

“Ba wanda zai iya ba ku cikakken bayanin abin da ya faru tsakanin sojoji da ‘yan bindiga a yanzu. Za mu iya samun cikakkun bayanai game da haduwar ne kawai idan an gama fadan.

“Muna fata a karshe sojoji za su fatattaki ‘yan bindigar. Addu’armu ita ce, Bello Turji ya kasance cikin wadanda za a kashe a yakin.”

Wata majiya, wadda ita ma ba ta son a ambaci sunanta, ta ce, “Wannan ita ce karo mafi muni tsakanin sojoji da ‘yan fashi da muka gani a wannan yanki. Ba mu taba ganin irin wannan yaki a wannan garin ba. Muna fatan wannan shine karshen Bello Turji.

“Fatan mu shi ne a tura karin sojoji yankin domin tallafa wa wadanda ke kasa. Na tabbata ‘yan fashin kuma za su yi kira da a karfafa musu gwiwa daga abokan aikinsu.”

Ko da yake ana zargin Turji yana zaune ne a cikin dajin da ke karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zmafara, amma ikonsa ya bazu zuwa kananan hukumomin Sabon Birni, Isa da Goronyo a Sokoto.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button