Ana ci gaba da jiran sakamakon zaɓen yankin Somaliland da aka yi a jiya Laraba

Spread the love

Ana ci gaba da jiran sakamakon zaɓen yankin Somaliland bayan kaɗa ƙuri’a a jiya Laraba, zaɓen da ke da fatan share hanya ga fatan yankin na samun ƴanci, fiye da shekaru 30 bayan ɓallewa daga Somalia.

Tun a shekarar 1991 ne yankin na Somaliland ya ɓalle daga Somalia tare da ayyana kansa a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta, sai dai har zuwa yanzu babu ko ƙasa guda da ta amince da halascinsa, rashin karɓuwar da ya haddasawa yankin gagarumin koma baya a wani yanayi da rikicin ƙabilanci ke ci gaba da tagayyara shi.

Somaliland mai yawan jama’a miliyan 7 da ke a yanki mai matuƙar muhimmanci lura da yanda ya yi iyaka da tekuna biyu da suka ƙunshi Indian Ocean da kuma Red Sea, na fama da matsanancin talauci, sai dai yankin na da yaƙinin cewa nasarar iya gudanar da sahihin zaɓe a wannan karon ya taimaka musu wajen samun goyon bayan wasu ƙasashe.

Al’ummar yankin na cike da fatan sabon shugaban Amurka Donald Trump, ya taka rawa wajen amincewa da ƴancin yankin don samun goyon bayan ƙasashe.

Ko a bara yankin na Somaliland ya kulla yarjejeniya da Habasha, ta yadda ƙasar za ta riƙa amfani da gaɓar ruwan yankin da nufin samun amincewar Addis Ababa da yankin a matsayin mai cin gashin kansa a tafarkin diflomasiyya.

Tun a shekarar 2022 aka shirya gudanar da zaɓen yankin na Somaliland, amma majalisar yankin ta tsawaita wa’adin shugaba Muse Bihi Abdi wanda a yanzu ma ya ke fafatawa da ɗantakarar bangaren adawa Abdirahman Cirro a zaɓen na jiya, da bayanai ke cewa an gudanar da shi cikin luma ba tare da hatsaniya ba.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button